Translations:On Yedinci Söz/359/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Allah, wanda yake shi ne mai Rahama mai jin ƙai, wanda kuma yake shi nc mai hikima, mai ba kowa, ya halitta wannan duniya ne, kai ka ce domin mutane su zo su sheƙe ayarsu, saboda irin abubuwan da Allah ya sa a cikin duniya na ƙawace ƙawace, domin jin dadin ɗan Adam.

    Allah ya kawata ɗan Adam, ya kuma tufatar da shi, sannan ya sa masa ji da gani ya yi masa dai komai da ya dace da shi.