Translations:Yirmi Üçüncü Söz/192/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Idan kuwa muka duba fuska ta biyu ta ɗan adam, za mu ga cewa duk da rauninsa da kasawarsa, Allah ya ɗaukaka kuma ya daraja ta mutum. Saboda shi Allah maɗaukaƙi shi ne ya halicci mutum da rauni da kasawa, saboda mutum ya san akwai fa wanda yake da iko da shi. Mutum ya san fa akwai mai tabbacin karfi mai Rahama, wanda karfinshi da ikonshi da ƙyautar Shi ba su da iyaka.