Translations:Yirmi Üçüncü Söz/201/ha
Daga nan sai na bar wurin, na zo na tambayi labarin waɗannan wurare. Sai aka ce mani, wancan wuri na farko inda ga mutane waje amma ciki fanko, wuri ne na kafirai tsantsa. Amma wuri na biyu inda na ga mutane a kintse cikin natsuwa, wuri ne na Musulmi tsantsa. Sai kuma na iso wani wurin. sai naga an rubuta suna a wani katon gida ko in cc fada kamar haka: (SAID). Ba sai na ruɗe na duba, na duba. na sake dubawa, kai sai da ta kai kamar ina ganin kaina a ciki sai kawai na farka.