Translations:Yirmi Üçüncü Söz/247/ha
Haka kuma, idan mutum ya kalli sama, nan ne zai tabbatar masa da kaɗaituwar Allah, da kuma ikon sa, saboda abubuwa dake ciki irin su taurari, wata, giza-gizai da sauransu. Wannan zai ƙara maka yarda da imani da mika wuya da ƙara jawuwa ga bauta da haƙiƙancewa da kuma ƙara kaɗaita Allah.