Kira Ga Mutanen Littafi
Muminai sun yi imani da abinda aka saukar maka, da abinda aka saukar kafinka kuma suna da yaƙini da Jahira”
Kur’ani 2:4
Game da cewa “sun yi imani da abinda aka saukar kafinka” to kamar cewa da ake ne:
“Ya ku mutane, kamar yadda” ku ka yi imani da kur’ani, to ku yi imani da hitattafan da aka aukar kafinku, domin kur’ani shaida ne a kan kasancewarsu saukakku daga Allah”.
Kuma wannan magana, za ta iya karɓar wannan fassarar. “ya ku mutanen littati (yahudu da Nasara)! Kamar yadda ku ka yi imani da annabawan farko, da kuma litattafan farko, to ku yi imani da annabi Muhammadu (SAW) da kuma kur’ani. Domin kamar yadda (waɗancan annabawa da litattafai) suka ba da labarin zuwanasa, za ku ga haka a wajen annabi Muhammad (SAW) da kuma cikin kur’ani. Saboda haka kenan, sai ku yarda tare da amincewa cewa kur’ani Maganar Allah ne, kuma annabi Muhammad (SAW) Manzon sa ne.
Musulunci, wanda masominsa kurani, (wanda shi kuma an sauƙar da shi a cikin wani lokaci mai albarka), kamar wata bishiya ce wadda tushenta, shi ma ya samu kafuwa ne a wani lokaci mai albarka. Jijiyoyin wannan bishiya sun watsu ko’ina saboda ruwa da suke samu wanda yake raya da su. Rassan wannna bishiya kuma sun miƙa sun isa wuri mai nisa, samar da ya’ya suke har zuwa wannan zamani namu. Kai! A karkashin shika-shikan Musulunci, akwai shckaru aru aru da suka shige, akwai kuma shekaru aru aru masu zuwa, lura da su da amfani da su, zai wanzar da zaman lafiya.
Wajen kiran mutanen littafi su amshi Musulunci. kur’ani ya yi bayaninsu a wata aya. Ga dai abinda ayar ke nufi tare da bayani.
Yaku mutanen littafi! Babu wata wahala gare ku, ku amshi musulunci. Kada ku gan shi, kamar wani abu mai wahala. Saboda ko kur’ani bai ce ku yi watsi da addininku ba, cewa kawai ya yi ku cika imaninku, sanna ku dora a kan abinda na ke tare da ku/na addini.
Saboda ku duba, kur’ani fa ya ƙunshi ƙyawawan koyarwa na litattafan farko. Shi ku’rani bai zamo ba face mai bayani da daidaitawa. Kuma a matsayinsa (kur’ani) wanda ya zo da dokoki, babu abinda ya canza (na dokokinku) face ‘yan abubuwa kaɗan, su ɗm ma saboda, sauyin lokaci da zamani da kuma Muhalli (wato wuri), wanda a wannan lokaci yin haka babu wata illa ciki. Canzawar yanayi ke da wuya, sai abinci da tufafi da kuma sauran abubuwa su ma su canza. To haka ma rayuwar ɗan adam take, da cewar ya samu kansa a wani canji a yanayin rayuwarsa, to kusan duk al’amuransa sai su canza, yadda zai dace da zamani. Wani lokaci, sai ka samu abu na da matuƙar amfani; wani lokaci ko, sai ka iske abin nan ya zama mai cutarwa misali, an ce “abincin wani, gubar wani.” To saboda irin waɗannan abubuwa yake sa Allah ya kawo ko ya canza wasu dokoki (waɗanda aka sani zamanin wasu annabawan) ya kawo wasu (a lokacin Annabi Muharnmadu (SAW). Ma’ana lokacin waɗancan dokoki ya wuce, yanzu, sai a ci gaba da amfani da waɗandaAllah ya saukar!
Allah ya sa mu dace: wassalam Alaikum warahmatullahi wa barakatu.