Translations:On Yedinci Söz/371/ha
Hanya ta hudu: haka nan hasken imani kan sa mutum ya fahimci mutuwa fa ba wai yinta ake yi haka nan ba, a’a, musayar wurin zama ne daga wannan wuri zuwa wancan. Kuma kabari ba wai rami ba ne kawai mai duhu, a, a, wuri ne mai haske, duniya kuwa (duk da ƙyale ƙyalenta), kurkuku ne in an ƙwatanta da lahira.