Translations:Yirmi Üçüncü Söz/148/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Imani, haske ne kuma ƙarfi ne, ba shakka, wanda yake da ƙwaƙƙwaran imani, to zai iya ja da duk duniya, kuma ya jure wa duk wani matsi gwargwadon imaninsa. Yana faɗin cewa: “Na dogara ga Allah to haka, zai ta gudanar da rayuwarsa babu abunda zai same shi. Duk wanda ya miƙa komai zuwa ga Allah mai cikakken iko, haka zai ta tafiya cikin rayuwa a cikin sauƙi har ya gama da rayuwa matabbaciya, daga nan sai aljanna, domin jin daɗin na din din din. Amma ga wanda bai wakkala komai zuwa ga Allah ba, maimakon rayuwa mai sauƙi sai ya faɗa cikin wahala, ya koma mafi ƙasƙantar maƙasƙanta. Muna iya cewa imani, shi ke haifar da kaɗaita Allah, kaɗaita Allah kuma, shi ke haifar da miƙa wuya ga Allah, miƙa wuya kuma shi ke haifar da dogaro ga Allah wanda shi kuma, shi ke haifar da rabauta a lahira.