Translations:Yirmi Üçüncü Söz/182/ha
Ɗan adam yana wani matsayi na buƙatar komai na duniyar nan wanda ke da ɗangantaka da shi. Bukatun mutum ba su da iyaka. Yadda yake son rani haka yake soo damina. Yadda yake son mazauni, haka yake buƙatar aljanna maɗauwamiya. Haka kuma yadda yake son ganin wani aboki nasa, haka, yake son ganin Allah maɗaukaki mai rahama, kuma kamar yadda yake son ziyartar wani masoyi (nasa) haka yake so Allah ya biya nasa bukatunsa, domin saduwa da abokansa da ya rasa; haka kuma akwai buƙatar mutum ya nemi tsaro ga mai maɗaukakin karfi. Saboda kuwa shi ne mai jinkintarwa a duniya, sai a lahira ya ba da, wannan yana daga cikin abubuwan ban mamaki nasa, kawar da wannan duniya, ya maye ta da ta lahira.