Translations:Yirmi Üçüncü Söz/185/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Haƙiƙa, ya kai mutum kana da fusƙoƙi guda biyu: fuska ta farko ita ce matsayinka na abin halitta, akwai ka da sanin abu mai kyau, da kuma ɗaukan matakin da ya dace, da kuma bin hanyar gaskiya. Fuska ta biyu kuma ita ce ta ɓarna, da ko-in-kula, da mugunta da kuma son-rai.

    Idan muka ɗauki fuska ta farko, za mu ga cewa akwai ka da rauni, idan ko muka dubi fuska ta biyu za mu ga cewa, ka kere ƙasa da tsauni, kai har ma da samaniya, ka ɗaukar wa kanka kayan da ya fi nasu. Duba Kur’ani 33:72 me yasa haka?

    Dalili kuwa shi nc, a duk lokacinda ka aikata wani aiki ƙyaƙƙyawa ka yi shi ne ko kuma ka aikata shi ne gwargwadon karfinya da iyawar ka. Amma a duk lokacin da ka aikata wani mummunan aiki to muninsa da ɓarnarsa watsuwa suke sai illa-masha Allah.