Translations:Yirmi Üçüncü Söz/186/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Kafirci cuta ce kuma barna ce, kuma musuntawa ce ga samuwar Allah. Wannan mugun abu (kafirci) ƙaskantuwa ne ga halittun duniya gaba ɗaya, tozarci ne ga sunaycn Allah (mai girma) kuma cin zarafin ɗaukacin bil-adama ne. Saboda kuwa su sun kai wani matsayi na ɗaukaka. Amma kafirci ya musunta haka, ya maida su wasu abubuwan wasa waɗanda (wai) suke samammu tun fil- azal. Ya maida halittun Allah wani matsayi na cewa idan sun mutu, sai su ruɓe, shi kenan! Yin haka tozarci ne ga siffofin Allah da halittunsa waɗanda ya samar kuma ake iya gani. Kafirci yakan sa mutum ya zama raunanne, abin tausayi, maƙaskancin makaskanta, a cikin “yan adam. Saboda me, saboda kuwa mutum a matsayinsa na kalifar Allah a bayan ƙasa wata alama ce dake bayyana siffofin Allah wanda Allah cikin hikimarsa ya ɗaukaka zuwa wani matsayi maɗaukaki, wanda ya haye kasa kanta, ya kuma fi duk wani tsauni tsawo, har ya kai ga samun ɗaukaka fiye da mala’iku, Kafirci, yakan maida mutum wata halitta, mara amfani.