Translations:Yirmi Üçüncü Söz/199/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Wai wata rana ne zan shiga wani babban gari, sai na ga wani babban wuri. A gaban wannan wuri ana ta biki, kusan hankalin kowa ya koma wajen bukin. Sai na duba, sai na ga shugaban wannan wuri, yana tsaye a wata kofa yana wasa da kare. Ga mata nan kuma ko ina tare da samari ana tattaunawa; ya yin da manyan mata kuma ke ta dawainiyar daidaita yara. Mai kula da shigi da fice kuma, yana kan aikinsa. Sai na lura na ga cewa can cikin wannan wuri, ba komai. Ba abinda ke faruwa a ciki, abinda ya kamata a yi a cikin ne ake yi a bakin ƙofar wannan wuri. Kai da ganin mutanen wannan wuri ka san abinda ake kira ɗa’a ya yi musu kaɗan, shi yasa suke lalacewa a wannan wuri.