Translations:On Yedinci Lem'a/195/ha
Ka ga dai ka shuka su wari ɗaya ƙasa ɗaya sun sha ruwa iri ɗaya, ɗumi da hasken rana iri ɗaya, amma me? Mai zaƙi, zai yi zaƙin sa, mai ɗaci ma haka, mai koren ganye ya yi kore, mai ja ya yi ja da dai sauransu. Kuma amma ga shi duk abu ɗaya suka yi amfani da shi, kafin su fito, waye ya yi wannan aiki?