Translations:Yirmi Üçüncü Söz/176/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Wata addu’ar kuma ita ce wadda muke yi, mu mutane. Wani lokaci, mukan roki Allah da bakinmu da kuma zuciyoyinmu. Mukan yi waɗannan addu’o’i ne domin samun wasu abubuwa da mu kanmu ba za mu iya samu ba. Abin faranta rai mai yin addu’ar ya san akwai mai sauraron sa, ya yi imani da cewa lallai akwai wanda ya san abinda ke cikin zuciyarsa, wanda zai iya biya” masa kowace irin buƙata tasa. Irin wannan addu’a takan samu karbuwa a mafi yawan lokuta, tunda dai ana yinta ne kai tsaye, zuwa ga mai kyauta mai Rahama, Mafi tausayin bayinsa, mai kawar musu da dukkan rashi.