Translations:Yirmi Üçüncü Söz/177/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Saboda haka, ya kai mutum mabukaci, kada ka yi watsi da yin addu’a wadda ita ce hanyar kaiwa ga taskokin rahama da kuma karfin da ba ya ƙarewa. Miƙe tsaye, ka rike shi ƙwarai, ko ka samu kaiwa ga kololuwar ɗaukaka ta’yan adam. Rika sa kowa da kowa a cikin addu’arka. Rika cewa “Gare ka kawai, muke neman taimako” (ba gare ka kawai nake neman taimako ba); ka kasance mafi kyaun abin kwatance na halitta.