Translations:Yirmi Üçüncü Söz/183/ha
Saboda haka ga mutum dake wannan matsayi abin bauta na gaskiya kawai shi ne Allah, wanda a hannunshi taskar komai take, wanda kuma babu wani abu mai ɓoyuwa a gare shi, ya gane ko ina da saninsa, shi baya buƙatar wurin zama, ya baranta daga dukkan rauni, babu kasawa ko nakasa a gare shi. shine Mai tabbataccen karfi, Maɗauƙaƙi Mai Rahama, kuma Shi ne Mai hikima.