Translations:Yirmi Üçüncü Söz/184/ha
Saboda haka ya kai mutum, idan kai bawa ne na Allah to za ka samu babban matsayi fiye da sauran halittu. Amma idan ka kauce, ka daina bautarsa, ka kama bautar waninsa, to ka zama bawan raununan halitta. Haka kuma idan ka bi son ranka, ka yi watsi da dogaro ga Allah da kuma rokonsa ka shiga alfahari da cika baki, to sai ka ƙasƙanta ka koma kasa fiye da yadda kiyashi ko kuɗan zuma idan an ƙwatanta su da sauran halittu, sai ka fi kuda ko gizo-gizo rauni. Haka kuma sai ka fi komai na duniya sharri da cutarwa. AUah ya tsare mu, amin.