Translations:Yirmi Üçüncü Söz/187/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    A takaice dai: Mutum wanda zuciyarsa ta yi kanta da barna da mugunta, zai iya aikata ɓarna wadda ba ta da iyaka. Saboda zuciyarsa ta riga ta dushc da barna. Zai iya aikata komai na barna, amma ya kasa aikata kaɗan na ƙyaƙƙyawa. Misali: a cikin rana guda, zai iya kada gini, amma ba zai iya tada wannan gini ba a rana guda. Amma idan mutum ya kauce wa son ransa, ya kuma nemi shiriyar Allah da gafararsa, to Allah zai shiryar da shi, kuma ya gafarta masa zunubbansa. Allah ya ce:

    “Waɗanda suka tuba, suka kuma yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, to Allah zai juya munanan ayyukansu zuwa ƙyaƙƙyawa.”

    Kur’ani 25:70.

    Mummunan aikin nan nasa mara iyaka, Allah zai juya shi zuwa ga kyakkyawan aiki wanda ba shi da iyaka. Zai kai ga ya samu matsayi na ɗaukaka.