Translations:Yirmi Üçüncü Söz/198/ha
Ci gaba, kamar yadda mutane suka ɗauka, ba shi ba ne ƙoƙarin samun jin dadin rayuwar duniya ta kowace hanya ta hanyar cuta, da maguɗi da yaudara da ɗai duk wasu dabaru da basu dace ba, wannan ba ci gaba ba ne - koma baya ne. Haƙiƙa na ga wannan wata rana a cikin mafarki.