Translations:Yirmi Üçüncü Söz/207/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    To idan mutum ya maida rayuwarshi ga son ransa, ya kasance burinsa shi nc ya more wannan rayuwa, wadda yake ta wani ɗan lokaci ce, sannan bayan haka ya koma ga Allah, to hatta Gaɓɓoɓin jikin shi sai sun bada shaida a kanshi.

    Amma idan har mutum ya fahimci cewa shi fa ba komai ba ne a wannan duniya na mai Rahama, kuma yana jin daɗi ne saboda ƙyautar da ya yi masa, to zai ji daɗi nan, kuma can ma kiyama yana da hutu da matsayi na ɗaukaka.