Translations:Yirmi Üçüncü Söz/230/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Eh! An ji kai ba koman ba ne, to amma ai an halitta ka saboda wani dalili na bautawa Allah sannan aka ba ka matsayi da basira da lura, da kalami, wanda kusan a ce, kai ne mai lura da komi na duniya kai ne mai lura da halittu, waɗanda a ko yaushe suke bauta da tsarkake Allah subhanahu wa ta’ala (SWA).