Translations:Yirmi Üçüncü Söz/234/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Ɗan Adam, an turo shi wannan duniya ne a matsayin halifa kuma baƙo, sannan aka ba shi iko iyakar gwargwaɗo. Sa’annan aka ba shi wasu aikace- aikace daidai iyawarsa. To saboda mutum ya aiwatar da waɗannan aikace aikace, sai kuma aka yi masa bushara da aljanna da kuma gargadi da wuta.

    A nan zan takaita bayani a kan aikin da aka ɗora wa mutum na bauta na riga na yi dogon bayani akan haka a wani wuri amma saboda a Kara fahimtar abinda nake cewa.