Translations:On Yedinci Lem'a/193/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    “To duk wanda ya aikata kyakkyawan aiki daidai da ƙwayar zarra, zai gan shi. Kuma duk wanda ya aikata aiki na shari (Mummuna) dai dai da ƙwayar zarra, zai gan shi”. Kur’ani 99:7-8.

    Wannan aya tana nuni ga tabbatar da kasancewar Allah mai lura da kiya-ye dukkan komai. Idan kana son sanin haƙiƙanin wannan ƙauli (magana) ta al-kur’ani mai girma, to ka duba shinfidar sama yadda Allah ya kiyaye ta Taurari ba sa karo, wata da rana ba sa cin karo, komai na ta fiya cikin tsari. To wanda ya tsara kuma ya kiyaye sama daga duk wani rudani, shi ne zai kiyaye aikinka, komia daɗewa za ka gan shi.