Translations:On Yedinci Söz/365/ha
Bayan wannan, kuma rahamar Allah a kusa take (ga bayinsa). kamar yadda cikin rahamarsa yake sa wasu su samu shahada a lokacin jihadi, kuma kamar yadda ragon da aka yi hadaya da shi don Allah, zai ceci mai shi a wurin tsallake siraɗi, haka kuma Allah yake sakawa duk wani bawa na shi wanda ya mutu yana wani aiki da Allah ya ɗora masa. Allah shi zai sakawa kowace rai abinda ta cancanta, sannan in yaso ya ƙara mata. Kuma rai wadda ta yi aikin ƙwarai ba za ta yi baƙin ciki ba, kuma ba za ta sha wuya ba, a lokacin komawar ta ga Allah.