Translations:Yirmi Üçüncü Söz/158/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Akwai dubban hujjoji da za su tabbatar da wannan Magana; ɗaya daga cikinsu ita ce samar da halittar mutum da dabba a wannan duniya. Bambancin halittu biyun shi ne imani. Mutum ya samu matsayinsa na mutumtaka ne ta hanyar imani. Ita dabba kan zo duniya ne tare da fahimtar wasu abubuwa, kuma cikin ɗan lokaci kaɗan sai ka ga ta fahimci komai da komai. Ɗauki misali ga mashinllera (wato tsettsewala) Wata tsuntsuwa ce da kuma kudan zuma waɗanda cikin ƙwana ashirin da zuwansu duniya, sai kaga sun fahimci komai amma mutum sai bayan ya shafe shekaru ashirn sannan ne zai fara fahimtar abubuwa.