Translations:Yirmi Üçüncü Söz/161/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Saboda haka, babban aikin mutum shi ne neman ilmi, da sanin yadda zai bautawa Allah, tare da miƙa wuya a gare shi. Ma’ana mutum ya tambayi kansa: “Cikin rahamar Allah waye ke gudanar da rayuwata haka’.’ Alheri da baiwa da na samu har na kawo wannan lokaci, wane ne ya yi mani su? ‘Waye ya raine ni, tun ina cikin rauni, har na kawo wannan lokaci?”

    Dole ne mutum ya san wa ya halicce shi ya kuma samar masa da waɗannan abubuwa, ya kuma miƙa wuya a gare shi, a cikin halin rauni ko cikin halin rashi; dole mutum ya fuskanci Allah da buƙatunsa. Kuraa (ya yi ƙoƙari) ya kai ƙololuwar bautar Allah a halin rauni da kuma talauci.