Translations:Yirmi Üçüncü Söz/171/ha
Haka kuma abinda yake a zahiri kamar yadda ayoyin ƙur’ani suka nuna. Shi ne cewa kamar yadda kowace abin halitta take bauta da-tsarkake Allah, haka kuma yake rokon (yin addu’a ga Allah.) Sukan yi haka ta hanyar da Allah ya hore musu, (kamar tsirrai da dabbobi) ko kuma ta baka (kamar mutane da aljannu) halittu sukan yi addu’o’i su roki abinda bai yiwuwa su samu sai ta hanyar rokon Allah, Ubangijin kowa da komai. Ƙowane abu mai rai yakan tsinci kanshi wani lokaci cikin ƙaƙa ni-ƙayi ko kuma neman kaucewa wani abu, ta haka sai ka ga yana neman tsari daga wurin Ubangiji mai Rahama.