Translations:Yirmi Üçüncü Söz/209/ha
Idan har za ka kwatanta irin baiwar da Allah Ubangiji ya yi wa ɗan adam ta wurin halitta da kuma wadda ya yi wa dabbobi, za ka ga cewa ɗan adam ya tsere wa dabbobi nesa ba kusa ba. Amma ta wajen jin daɗi da more ƙirar da Allah ya yi wa kowanensu, sai aga dabbobi sun fi ɗan adam jin dadi da more ƙirar da Allah ya yi wa kowannensu. Saboda me?
Saboda shi ɗan adam akwai dokoki da ke jagorancin rayuwarsa. Akwai abin da zai tuna wanda ya wuce ya yi nadamarsa, akwai kuma abinda zai tuna wanda zai zo, ya shiga halin zan yi. Saboda haka idan ya wuce gona da iri ga yadda yake tafiyar da gaɓoɓinsa, to sai ya yi da-na- sani!
Dabba fa? Dabba ba suda wasu dokoki da suke jagorantar rayuwarsu. Babu wani tunanin da za ta yi na abinda ya wuce ta yi nadama; haka nan, babu wani tunani da za ta yi na abinda zai zo nan gaba, ta shiga wani hali. Ka gani ita abinda ta sani, shi ne ta samu ta ci to godewa, wanda ya ba ta shikenan.