Translations:Yirmi Üçüncü Söz/218/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Wucewarsa ke da wuya, sai al’amarni ya canza. Sai ga ni cikin jirgi. Sai na tsirata. Ga furanni masu ƙamshi ta kowane ɓangare. Abinka da wanɗa bai sani ba, sai na miƙa hannu zan ciro furannin nan. Miƙa hannu ke da wuya, ashe duk ƙaya ne jikinsu, saboda haka, sai suka kakkarce mani, hannu suna ta jinni. Sai mai kula da jirgi ya ce da ni:

    “Idan kana son furannin nan, kawo kuɗi in ba ka. Ka ga yanzu ga raunin da ka yi, gas hi kuma hukunci na jiranka, don ka yi kokarin dibar su, ba are da izini ba.”