Translations:Yirmi Üçüncü Söz/254/ha
Kuma: Ya Ubangiji, ka/yi ɗaɗin tsira da aminci ga annabi Muhammadu Masoyinka, haske ga al’umma, mafi darajar mutane kuma mafi ƙyaun mutane. Ya Allah, ina roƙonka ka cire mani tsoro, ka daidaita tuntubena, ka yaye mani baƙin ciki da haɗarna, ka kusantar da ni gare ka, kada ka sanya ni mai bin son rai, ya Allah ka kara mani sani. Ya Allah wanda yake Rayayye wanda ya wadatu da kansa, ya Allah wanda yake Rayayye, ya Allah wanda yake Rayayye kuma ya wadatu da kansa. Allah ka yi jin kai a gare ni, da abokaina, da kuma muminai. Amin! Ya mafi jin ƙan musu jin ƙai, ya mafi ƙyautar masu ƙyauta!