WANE NE BEDIUZZAMAN SAID NURSI KUMA WANE LIFFAFI NE RISALAN-NUR?

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden

    Badiuzzaman Sa’id Nursi baturke ne (mutumin kasar Turkiyya), wanda aka haifa a can gabashin ƙasar, a shekarar 1877, kuma ya rasu a shekarar 1960, yana da shekaru tamanin da uku, ya yi kyakkyawar rayuwa abin koyi, mai cike da gwagwarmaya da sadaukar da kai wajen ɗaukaka addinin Musulunci. Ya kasance mashahurin Malami a lokacin rayuwarsa, wanda samun kamarsa sai an tona, saboda shi ba wai kawai ya karantu ba ne, ga abinda ya shafi addinin Musulunci, a’a, gwani ne masanin ilimin kimiyya da fasahar wannan zamani. Wannan ya sa a lokacin ƙuraciyar sa ake masa lakabi da BADIUZZAMAN, wato “Abin Mamakin Zamani”. Wannan duk saboda tsabar ƙoƙari da basira da Allah ya ba shi.

    Rayuwar Badiuzzaman ta bi ta goman karshe na daular Usmaniyya, wadda ta ruguje, bayan yaƙin duniya na ɗaya. Faɗuwar daular, ya sa a shekarar 1923, aka kafa mulkin jamhuriya, wadda a cikin shekaru talatin (1923-1950) ƙawai da kafuwarta, ta yi ƙaurin suna wajen gallazawa da nuna ƙiyayya ga manufofin addinin Musulunci.

    Shekarun da suka biyo bayan yaƙin duniya na farko, rayuwar Badiuzzaman ta kasance gwagwarmaya a kan ɗaukaka addinin Musulunci a dukkan fanni na rayuwaƙoƙarinsa, ba wai ya tsaya ba ne kawai ga karantar da ɗalibai da kuma muhawara da manyan malamai na ƙasashen Musulmi, kai ta kai ma ga jagorantar rundunar sa-kai, wadda ta fafata da sojojin mamaya na kasar Rasha waɗanda aka girke a gabashin ƙasar Turkiyya a 1914, inda bayan kusan shekaru biyu ana wannan fafatawa, aka kama shi a matsayin fursunan ya ƙi. Kai daɗin ɗaɗawama ya nemi yaɗa manufofin Musulunci ta hanyar cusa kai ga harkar rayuwa ka’in da na’in. Sai dai kuma shekarun da suka biyo bayan rikiɗewar daular Usmaniyya zuwa ga jamhuriya, su ne kuma suka sauya rayuwarsa zuwa wata rayuwa ta daban. Wannan kuwa ita ce keɓatuwa da kuma mayar da hankali ga karancc-karancc da ibada da kuma nazarcc-nazarce, saboda “in kiɗa ya canza, sai rawa ma ta canza.”

    Duk da yake Badiuzzaman bai taka wata rawa ba, a borin da aka yi wa gwamnati a 1925, kai bar ma kokarin shawo kan shugabannin boran ya yi cewa kada su yi wannan bore, amma duk da haka bai tsira ba, sai da gwamnati ta tura shi gudun hijirar karfi da yaji zuwa ƙasar Anatoliya. Shekaru Ashirin da biyar da suka biyo baya haka, rayuwar Badiuzzaman ba ta haɗu da komai ba face gallazawa, da cin zarafi da kuma ƙuntatawa daga hukumomin gwamnati. A waɗannan shekaru nena uzzurawa da yasarwa Badiuzzaman ya rubuta littafi mai suna “Risalan-Nur” ma’ana: Haskakkun Takardu, a kuma cikin waɗannan shekaru ne aka rarraba wannan littafi zuwa kowane lungu na kasar Turkiyya. Ga abinda shi Badiuzzaman yake cewa, bayan kammaluwar littafi:

    “Hakiƙa, yanzu ne na gane cewa, rayuwata ta kasance ne a wani yanayi na fahimta da hangen nesa, wanda ya jawo samar da wannan littafi don fahimtar al’kurani. Kai ka cc ma rayuwata a matsayin manazarci ta kasancc sharar fage ne ga waɗannan rubuce-rubuce wanda wannan, yaa nuna irin mu’ujizar Kur’ani.”

    Badiuzzaman ya gano babban dalilin da ya sa Musulunci ke durƙushewa, yake kuma ƙara rauni a duniya. Wannan dalili kuwa shi ne na raunin imani da manyan rukunan addinin Musulunci. Wannan, da kuma soki -buruntsu daga “yan duniya-muka-sa-gaba,” da mushirikai da wasunsu masu da’awar ilmin ƙimiyya da ci-gabaa karni na sha tara da na ashirin, ya sa shi Badiuzzaman fahimtar cewa, akwai bukatar ƙarfafa da kuma ceton imanin al’umma daga taɓarɓarewa. Abin yi shi nc, mayar da hankali wurin farfaɗo da addini tun daga tushcnsa, da kuma ƙarfafa imani, haka nan da mayar da martani ga duk wata suka, ba ta hanyar fito-na fito-ba, ko cacar baka.

    Saboda haka, a cikin shekarunsa na gudun hijira, Badiuzzaman ya rubuta gundarin littafm Risalan-Nur inda ya yi bayani, ya kuma fidda manyan rukunan imani, ya kuma yi bayanin haƙiƙancin alkur’ani, ga mutumin yau. Hanyar da na - bi kuwa ita ce ta rarrabe abinda ake kira imani da kuma abinda yake akasin imani don nuna ƙwaƙƙwarar hujjar kur’ani ta tabbatar da samuwar Allah da kaɗaitarsa da kuma annabta da tayar da matattu, wanda wannan na tabbatar da samuwar ɗan-adam da kuma wannan duniya.

    Ta haka, Badiuzzaman, ya bi hanya mafi sauki da kuma hujjoji ƙwarara, ya nuna cewa bayyanar binciken masana ƙimiyyar wannan zamani cike suke da ruɗu da kuma rikitarwa. Haƙiƙanin gaskiya shi ne, a cikin littafinsa na Risalan-Nur, Badiuzzaman ya tabbatar da gane yadda duniyar nan ke juyawa ta hanyar ilmin kmiyya yana tabbatar da ƙarfafa gaskiyar addinin Musulunci.

    Muhimmancin wannan littafi na Risalan-Nur ba ya lisaftuwa, saboda a cikinsa ne, Badiuzzaman ya sake farfaɗo da addinin Musulunci a cikin kasar Turkiyya a cikin wani lokaci da ƙasar ke fuskantar dushewa a cikin tarihinta. Daɗm-ɗaɗawa, wannan littafi na Risalan-Nur, ba wai kawai zai iya shawo kan matsalolin dake damun Musulmi ba ne kawai, zai ma iya magance matsalolin dake damun ‘yan adam gaba ɗaya. Wannan ko duk saboda dalilai da dama: Na farko rubutun littafm ya tafi daidai da tsarin tunani na mutanen wannan zamani, ta yadda mutum Musulmi ne ko ba Musulmi ba, littafin ya amsa masa tambayoyin da ke bakinsa ko zuciyarsa, haka nan ya kore masa shakku da ruɗu da shi ɗan-adam ya samu kansa a ciki.

    Haka nan kuma. Littafin ya yi bayani da warware abubuwan da suka shafi imani, wanda a da sai manyan malamai ne kawai ke nazari da kuma fahimtarsu, amma yanzu, kowa da kowa na iya nazari da fahimtar wani abu, ba tare da wahala ba.

    Dalili na gaba kuwa shi ne wurin yin bayanin haƙiƙanin dalilin kasancewar ɗan adam a wannan duniya, a cikin Risalan-Nur an nuna cewa kyakkyawar rayuwa a duniya da lahira za ta samu ne kawai ta hanyar imani da kuma sanin Allah, ya yin da baƙin ciki da takaici wanda rashin imani ke haifarwa, ke jiran marasa shi.

    KARKACEWA:

    Alkur’ani mai girma, ya jawo haƙalin mutum ta kowane hali na sa, shi ɗan adam ɗin. Ya jawo hankalin sa ga halittar duniyar da abubuwan da ke tafiya a cikin duniya, da kuma dalilin samar da halitta, kuma mutum ya san haƙƙin mahaliccin sa a kansa, a matsayinsa na ɗan adam.

    Irin wannan hanyar jawo hankali ta alkur’ani, ita ce Badiuzzaman ya yi amfani da ita a Risalan-Nur. Ya yi bayanin hakikanin yadda yanayin duniya yake, wanda ke nuna cewa akwai mahaliccinsu ta hanyar kawo ƙwararan hujjoji.

    Babban abin nema da bukata ga ɗan adam shi ne addini da kuma bukatar sani da bautawa, da miƙa wuya da biyayyarsa ga dokokinsa, waɗanda ya saukar ga Annabawansa. Wajen yin bayanin saƙon alkur’ani, wanda ma’aiki (SAW) ya kawo ya kuma yi bayani, kuma yin bayanin Musulunci wanda shi ne cikakkc kuma kammalallen addini ga ɗan adam, Badiuzzaman ya nuna a cikin littafinsa na Risalan-Nur cewa, babu wani saɓani tsakanin ilmin ƙimiyya da addini, maimakon hakan ma, samun ci-gaba da samun kyakkyawar rayuwa kan samu ne kawai ta wannan hanya (addini da ilmin ƙimiyya) wato hanyar addini.