Wasika ta Uku
Da sunansa. Tsarki ya tabbatar masa. Shi ne wanda babu wani abu face yana yabon sa da tsarkake shi.
(Ɓangaren Wasikar Na Badi’uzzaman Rubuta Ga Ɗaya daga cikin Dalibansa)
A cikin ɗaya daga cikin wasiƙunka, ka rubuta cewa kai ma kana son ka ƙaru da tunanina. To saurara, ga ɗaya daga cikin dubu na tunanin nawa.
Wani dare, a ya yin da nake bisa can kan kololuwar bene, sai na ɗaga kai na dubi halittar sama cike da taurari, sai ayar nan ta faɗo mani “To ba sai na yi rantsuwa da taurari masu tafiya ba “Masu gudu suna buya. Da dare idan ya ba da baya Kur’ani 81: 15-17
Wannan (aya) na nuna fasahar alkur’ani. Ayar tana magana ne a kan taurari waɗanda wani lokaci na dare su bayyana; wani lokaci kuma (na yini) su ɓuya.
Su waɗannan taurari, waɗanda babbarsu ita ce rana, sukan nunawa mai kallo cewa, haƙiƙa a bisa wani tsari mai ma’ana suke. Wani lokaci mai kallo zai gan su ga su nan bir jit! Babu wadda ta fi wata. Wani lokaci kuma sai ka gansu wasu sun fi wasu haske ko girma. Wani lokaci idan dare ya yi duhu (ba farin wata) haka za ka ga taurari sun haskaka sararin samaniya. Amma da cewa alfijir ya keto, haka za ka ga suna ɓacewa (buya) ɗaya bayan ɗaya.
Wannan ga mai tunani yana nuna girma da ɗaukaka da kuma hiƙimar wanda ya halicci wannan duniya tamu.
Daga nan, mutun zai iya fahintar cewa, haƙiƙa ba ƙaramar karramawa ba ce, ba kuma ƙaramar ɗaukaka ba ce, a ce mutum ya samu kusantar mai wannan aiki ta wurin imani da bauta masa, kuma har a, ce ga shi ka zama bakonsa. Wai!
Sonra kamere baktım. وَال۟قَمَرَ قَدَّر۟نَاهُ مَنَازِلَ حَتّٰى عَادَ كَال۟عُر۟جُونِ ال۟قَدٖيمِ âyetinin gayet parlak bir nur-u i’cazı ifade ettiğini gördüm. Evet, kamerin takdiri ve tedviri ve tedbir ve tenviri ve zemine ve güneşe karşı gayet dakik bir hesapla vaziyetleri, o kadar hayret-feza, o derece hârikadır ki onu öyle tanzim eden ve takdir eden bir Kadîr’e hiçbir şey ağır gelmez. “Onu öyle yapan, her şeyi yapabilir.” fikrini, temaşa eden her bir zîşuura ders verir.
Bayan da na gama kallon taurari, sai kuma na kalli wata na tuna da wannan ayar da take cewa.
“Kuma da wata, mun ƙaddara masa masaukai, har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino (ɗan karami) wadda ta tsufa” Kur’ani 36:39
Haƙiƙa, hasken wata, da tafiyar wata da kuma yadda take jujjuyawa dangane da yanayi, da kuma dangantakarta da rana, abubuwa ne masu ban mamaki.
Tambaya: wa ke tafiyar da wata, ya jujjuya ta ya kai, ta komo da shi?
Amsa: Allah shi ne ke wannan aiki. Tunda haka ne, to babu abinda zai kasance ya gagare shi babu wani abinda zai kasance ya zama mai wuya a gare shi.
Sonra هُوَ الَّذٖى جَعَلَ لَكُمُ ال۟اَر۟ضَ ذَلُولًا فَام۟شُوا فٖى مَنَاكِبِهَا âyeti hatırıma geldi ki zemin musahhar bir sefine, bir merkûb olduğunu işaret ediyor. O işaretten kendimi feza-yı kâinatta süratle seyahat eden pek büyük bir geminin yüksek bir mevkiinde gördüm. At ve gemi gibi bir merkûbe binildiği zaman kıraatı sünnet olan سُب۟حَانَ الَّذٖى سَخَّرَ لَنَا هٰذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُق۟رِنٖينَ âyetini okudum.
Lokacinda Duniya ke wannan gudu da ni, sai na ga kamar ana nuna mani sararin samaniya, ne ta cikin abin ka ko. Sai na ga ga taurari nan, kai ka ce sun yi sahu ne irin na mayaƙa (soja). A irin wannan wuri mai ƙyaun kallo, mutum bai san lokacin da zai rika furta: “Subhanallah!” Wato tsarki ya tabbatarwa Allah!
Daga nan sai wasu abubuwa guda biyu da suka shafi imani suka faɗo mani. Wadannan abubuwa sune:
Na farko shi ne tambayar da wani baƙona ya yi mani, wanda ke nuna cewa shi dai mai shakka ne.
Tambayar kuwa ita ce: “a ranar ƙiyama, cikin yarɗar Allah ‘yan aljanna zasu kasance sun tsallake siraɗi kamar walƙiya, sai su shiga aljanna. Wuta dai kowa ya san ta da nisa. To su ‘yan wuta ga su dauƙe da kaya niƙi-niƙi (na zunubi) yaya za su yi har su kai ga ita wutar?”
Abinda ya faɗo mani a rai shi ne, mu ɗauka mutane za su halarci, wani babban taro da aka gayyace su, kowannensu ya shiga jirginsa. Cewa na yi kowannen zai isa ne daidai da saurin jirginsa da sauri da rashin sauri, kowa dai zai isa. Ko ba haka ba?
Abu na biyu shi ne, Allah ‘ya yi karfm iko, mahaliccin kowa da komai, wanda shi kaɗai yake ba shi da abokin tarayya, saboda ya nuna cikar ikon sa da hiƙimarsa da kuma kadaitakarsa cikin mulkinsa, sai kaga da abu ƙalilan ya samar da abubuwa masu yawa, misali samar da halittu daga ruwa.
Kamar yadda na faɗa ne a cikin wasu kalmomi nawa kuma kamar yadda yake a kur’ani da dai a ce ba abu ɗaya ba ne (wato Allah) ya samar da halittu, to da an samu rikice-rikice da yawa.
Abin dubawa shi ne idan akwai shugabanni da yawa, to za lca samu cewa kowanne shugaba nashi Umarni yake so a bi. To Misali, ko da za a yi yadda kowane Shugaba yake so, sai ka iske an fuskanci wasu matsaloli, idan ba’a kai ga kwatsa yaƙi ba. Idan shugaba ɗaya ne, to za ka is’ke, komai na tafiya daidai, saboda shi ƙadai nc yana juya al’amuransa, yadda yake so.
Ka duba ka gani, da yake kaɗawar is’ka, tafiye, tafiyen rana da wata, yanayin rani da damina, sanyi da zafi, samuwar dare da yini, aiwatar da su yana zuwa ne daga wurin shugaba ɗaya (Allah), komai na tafiya daidai ba wahala ba mishkila. Shi yake yin yadda ya so da su, ya juya su, ya kaɗa su yadda har su sa mai kallo mamaki yadda ake dare da yini, da taurari da wata da rana suke juyawa, kuma a kullum haka, ba karkata, me yasa haka?
Saboda nashi ne, shi ke tafiyar da su yadda ya ga dama. Da ya so sai ya naɗa kasa, ta zama ita ce shugaba ga taurari, ya kuma maida rana a matsayin. Fitila kamar yadda take a yanzu, ta rika ba da haske da zafi ga halittarsa. Kuma ya maida rani, da damina, da sanyi. da zafi su ri ka kai da komowa dare da rana. Haka nan kuma dare da ranar waɗanda suke kwararan abubuwa masu nuna hikimarsa sai ya maida su ɗaya gabas daa yamma. Ma’ana ɗaya na gabas, ɗaya na yamma; idan kai gabas, sai ka shiga rana ko dare idan kuma kai yamma, nan ma, sai ka shiga rana ko dare, Kuma shi Allah, Shi ne ta cikin ikonsa, yake nuna wata a kullum ta fasali dabam- daban, ta yadda ɗan adam zai iya gane kwanan wata a kowace rana. Har wa yau, Allah shi ne ya ƙawata sammai da taurari waɗanda suke haske musamman a dare mai duhu ya kuma nuna cewa akwai wata hikima ta daban fa halittar taurari bayan kasancewarsu suna ƙawata sama.
To da a ce waɗannan abubuwa ba Allah ke tafiyar da su ba, da an samu ruɗani mai yawa tsakanin taurari da rana da wata da kuma duniyarmu.
To kasancewar nasara ga duk abinda abu ɗaya ke aiwatarwa, shi yasa ‘yan kasuwa ko masu masana’antu, kan haɗe su zama “tsintsiya maɗaurinki ɗaya.” Ga su dai da yawa, amma dunƙule suke, saboda abubuwa su tafi musu cikin sauƙi, daga nan sai ka ga kamfani ya samu.
A taƙaice dai, fanɗarewa kan haifar da wahalolin da ba su da iyaka, ya yin da akan samu cikakken sauƙi ta hanyar tauhidi Imani da kadaita Allah.
Mai Juriya, Shi ne mai uriya!
SAID NURSI
Kur’ani kiran ku yake, ku cika Imaninku, ba ku yi watsi da shi ba.