Translations:Yirmi Üçüncü Söz/142/ha
Ga Mafarkin:
Na yi mafarkin ga ni a kan wata gaɗa da aka gina a tsakanin wasu tsaunuka guda biya, waɗanda suke daura da juna. Karkashin gaɗar nan akwai wani kwari, mai tsananin zurfi. Ni kuma gani a kan gadan nan. Wani matsanacin duhu duk ya kewaye duniya. Dana duba dama na sai na ga wani katon rami mai tsananin duhu, na kuma duba hagu na naga gagarumin haɗari, ga kuma tsabar duhu. Na kuma duba ƙarƙashin gadar, na ga rami, wanda zurfinsa ba iyaka. Ina da wata tocila a hannuna mara haske. Idan na haska ina gani kaɗan. Sai na ga wasu abubuwan ban tsoro. Sai na ga dodanni da zakoki sun kewaye ni. Nan da nan sai na ce: “Kai tocilan nan ma dai bata hasƙaƙa mani komai.” Sai na wurgar da ita ƙasa na bi zan take. Takawar da zan yi sai na ga wuri ya yi haske, kai ka ce an kunna wata ƙatuwar fitila, ko’ina ya yi haske. Nan da nan komai ya koma kamanninsa.