Translations:Yirmi Üçüncü Söz/168/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden
    10.51, 23 Temmuz 2024 tarihinde Said (mesaj | katkılar) tarafından oluşturulmuş 136313 numaralı sürüm
    (fark) ← Önceki sürüm | Güncel sürüm (fark) | Sonraki sürüm → (fark)

    Haka nan addu’a, wata nau’I ce ta bauta, wanda sakamakonsa sai a lahira. Kowace addu’a tana da lokaci da kuma dalilin yinta. Misali: akwai salloli da addu’o’i da ake yi a lokacin fari, don samun ruwa. Akan yi su ne don bauta ga Allah, da kuma neman biyan buƙata. Idan aka yi su don samun ruwan kawai to ba za su samu karbuwa ga Allah ba, haka kuma kusufin rana da wata lokuta ne da ake sallolin kisfewar rana da wata. Waɗannan salloli ba wai ana yinsu ba ne don kawai rana da wata su fito, a’a, ana yin su ne domin bautar Allah.

    To haka ma sallar sha-da-fari, haka kuma addu’o’in da ake yi don yayewar wasu jarrabu da masifu, lokacinda mutum ke gane rauni da kasawarsa, sai ya yi addu’a da neman tsari ga Allah wanda ya mallaki dukkan (kuma ciƙaƙƙen) ƙarfi.