Translations:Yirmi Üçüncü Söz/224/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden
    20.42, 23 Temmuz 2024 tarihinde Said (mesaj | katkılar) tarafından oluşturulmuş 136741 numaralı sürüm ("Ɗan adam, a cikin duniya kamar dai, ɗan ƙaramin yaro mai. Rauni da kasawarsa, abubuwa ne da ba su misal to. Saboda ya kasance da waɗannan abubuwa biyu (wato Rauni da kuma kasawa) shi yasa ma aka mayar da shi abu mai rai domin idan da zai zama mara rauni kuma mai iya komai da kansa, to da zai kasance babu buƙatar a halitta shi domin a jarraba shi. To amma idan har ɗan adam zai fahimci shi raunanne ne, sannan ya mika wuya (wato ya roki buƙatarsa)..." içeriğiyle yeni sayfa oluşturdu)
    (fark) ← Önceki sürüm | Güncel sürüm (fark) | Sonraki sürüm → (fark)

    Ɗan adam, a cikin duniya kamar dai, ɗan ƙaramin yaro mai. Rauni da kasawarsa, abubuwa ne da ba su misal to. Saboda ya kasance da waɗannan abubuwa biyu (wato Rauni da kuma kasawa) shi yasa ma aka mayar da shi abu mai rai domin idan da zai zama mara rauni kuma mai iya komai da kansa, to da zai kasance babu buƙatar a halitta shi domin a jarraba shi.

    To amma idan har ɗan adam zai fahimci shi raunanne ne, sannan ya mika wuya (wato ya roki buƙatarsa) “bil-kauli, wal amali” bisa magana da kuma aiki to ba shakka da ya cimrna burinsa, haka kuma da zai fahimci kasawarsa, sannan ya nemi taimako ga Allah, to da ya kai ga cimma manufarsa cikin sauki.

    Amma me? A wasu lokuta, idan (aka biya) Allah ya biya wa mutum bukatunsa, sai shi mutum ya rika ganin kamar ko dabarunsa da kokarinsa ne ya kawo wannan abu alhali kuwa Allah ne, Mutum ya manta da haka.

    Ga wani misali: Kaza ta ican faɗa wa shirwa ko shabo, domin ta kare ɗanta wanda yake raunanne.

    Haka kuma, ɗan zakanya yakan ƙwace abinda uwarsa ta samo ya ci ya koshi, ita ko ta ƙwana da yunwa. Ka ga ai ba shi ba ne ya fita ya farauto uwarsa ce, amma ga shi ya ƙwata, wanda idan aka ce ya fita ya farauto ne, ba zai iya ba. To duka wannan rahama ce ta Allah, wanda ya kamata kowa ya sani.