Translations:Yirmi Üçüncü Söz/231/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden
    20.45, 23 Temmuz 2024 tarihinde Said (mesaj | katkılar) tarafından oluşturulmuş 136754 numaralı sürüm ("Saboda haka ya kai mutum, a matsayinka na abin halitta mai rai, kai fa ba ka zama komai ba, sai raunanne mabukaci, wanda yake mai rayuwa, kuma mai mutuwa. Allah ya yi maka baiwa ta hasken imani, da haskakawar ubangiji, ya samu ne ta hanyar Musulunci. Ka sani Allah ya ba ka wani matsayi na ɗaukaka, wanda bai ba wasu halittu nasa ba, to kamata ya yi a ce ka san haka, ba’a zuci ba kawai har ma ka furta da cewa: “Ubangijina mai rahama, ya sanya duniya..." içeriğiyle yeni sayfa oluşturdu)
    (fark) ← Önceki sürüm | Güncel sürüm (fark) | Sonraki sürüm → (fark)

    Saboda haka ya kai mutum, a matsayinka na abin halitta mai rai, kai fa ba ka zama komai ba, sai raunanne mabukaci, wanda yake mai rayuwa, kuma mai mutuwa. Allah ya yi maka baiwa ta hasken imani, da haskakawar ubangiji, ya samu ne ta hanyar Musulunci. Ka sani Allah ya ba ka wani matsayi na ɗaukaka, wanda bai ba wasu halittu nasa ba, to kamata ya yi a ce ka san haka, ba’a zuci ba kawai har ma ka furta da cewa:

    “Ubangijina mai rahama, ya sanya duniya ta zama gida gare ni, yana haskaka mani ita da rana da wata, ya kawata mani ita da furanni da shuke-shuke ta hanyar ruwan sama; ya sanya yanayi narani da damina don jin daɗina da sauran halittu” (Saboda haka nagode maka ya Allah).