Translations:Yirmi Üçüncü Söz/163/ha
Daɗin ɗaɗawa, tun da dai mutum, a kowane hali, kuma a kowane yanayi cikin jarabawa yakc daga fannonin rayuwa dabam daban ga rauni ga kuma bukatu nasa na yau da kullum, to bayan imani da ya yi sai kuma ya miƙa wuya ga Allah. Mika wuya, shi nc ainihin tushen bautar Allah. Dubi misaliqn yaro, idan yana buƙatar wani abu, yalcan yi kuka ne a ba shi, wani lokaci kuma ya tambaya, ma’ana, yakan yi nuni ko kuma ya yi Magana, sai kaga an biya masa buƙatarsa. Haka shi ma mutum a gaban Allah mai rahama mal jin kai, yakan yi kuka ne ga Allah ko kuma ya roki Allah ga abin da yake bukata, sai kaga (Allah) ya ba biya masa buƙatarsa. Amma kuma idan daga bayan ya samu ya fara tunanin cewa:
“Mene ne na damun kai, abinda bai kai in tayar da hankali ba, na zo ina tada hankalina, wannan abu dai, ko ta halin ƙaƙa zan samu, gani da dabaru kamar me?” ya dai nuna rashin godiya da tawali’u ga Allah, ta haka sai ka ga ya haɗu da matsananciyar azaba. Allah kiyashemu, amin.