Translations:Yirmi Üçüncü Söz/168/ha
Haka nan addu’a, wata nau’I ce ta bauta, wanda sakamakonsa sai a lahira. Kowace addu’a tana da lokaci da kuma dalilin yinta. Misali: akwai salloli da addu’o’i da ake yi a lokacin fari, don samun ruwa. Akan yi su ne don bauta ga Allah, da kuma neman biyan buƙata. Idan aka yi su don samun ruwan kawai to ba za su samu karbuwa ga Allah ba, haka kuma kusufin rana da wata lokuta ne da ake sallolin kisfewar rana da wata. Waɗannan salloli ba wai ana yinsu ba ne don kawai rana da wata su fito, a’a, ana yin su ne domin bautar Allah.