Translations:Yirmi Üçüncü Söz/211/ha

    Risale-i Nur Tercümeleri sitesinden
    14.01, 23 Temmuz 2024 tarihinde Said (mesaj | katkılar) tarafından oluşturulmuş 136571 numaralı sürüm ("Wani mutum da yaran gidansa guda biyu, sai ya ɗauki naira ɗari ya ba ɗaya ya ce ya sayo masa yadi, ya kawo naira dubu ya ba na biyun ya ce shi ma ya sayo masa yadi. Kowannensu ya tafi kasuwa. Mai Naira dari ya sayo kyakkyawan yadi; mai Naira dubu ko da yake wawane ya je ya mika kuɗinj kawai ga mai kaya ya ce ya ba shi yadi. Abinka da mutumin yau, ganin mai sayen yadi sakarai ne, sai mai kaya ya ɗauko yadin da ko kare baya sa ba ya ba shi. Wanda aka..." içeriğiyle yeni sayfa oluşturdu)
    (fark) ← Önceki sürüm | Güncel sürüm (fark) | Sonraki sürüm → (fark)

    Wani mutum da yaran gidansa guda biyu, sai ya ɗauki naira ɗari ya ba ɗaya ya ce ya sayo masa yadi, ya kawo naira dubu ya ba na biyun ya ce shi ma ya sayo masa yadi. Kowannensu ya tafi kasuwa. Mai Naira dari ya sayo kyakkyawan yadi; mai Naira dubu ko da yake wawane ya je ya mika kuɗinj kawai ga mai kaya ya ce ya ba shi yadi. Abinka da mutumin yau, ganin mai sayen yadi sakarai ne, sai mai kaya ya ɗauko yadin da ko kare baya sa ba ya ba shi.

    Wanda aka aika da Naira ɗari, yana zuwa, ga mai gidansa, sai yabo da san-barka. Mai Naira dubu kuwa, ai sai zagi da tsinuwa kai har ma da duka.

    Me yasa haka ta faru? Saboda ko sakarai ya san cewa, Naira dubu ta fi gaban ta kare a abinda ko kare ba zai ci ba.