KALMA TA ASHIRIN DA UKU DAGA
(WANNAN MAGANA TA KUNSHI BABI BIYU)
Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai jin ƙai
Haƙiƙa, mun halicci mutum cikin mafi kyakkyawan tsari. Sannan muka mayar da shi mafi raunin masu rauni. Sai dai waɗanda suka yi imani suka aikata aiki na ƙwarai.
Kur’ani, 95:4-6.
BABI NA ƊAYA
Za mu yi bayani a cikin hujjoji biyar; hujjoji biyar kawai daga cikin dubbai na Imani.
Hujja ta Farko
Ta hanyar imani ne, mutum ke ɗagawa ya kai wani matsayi na ɗaukaka wanda zai kai shi ga samun aljanna. Haka kuma ta cikin duhun kafirci ne, mutum ke zama mafi kaskantar maƙasƙanta, har ya kai ga ya faƙa wuta. Imani kan sadar da mutum ga mahaliccinsa, wanda wannan wata dangantaka ce. Ta haka, mutum zai samu ɗaukaka, da shiryuwa ta hanyar imani. Kafirci kan ɓata kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin mutum da mahaliccinsa, daga nan kuma ɗaukakar da zai samu za ta zama ta mutumtaka ce kawai. Kuma tunda wannan ɗin ma na wani dan lokaci ne (rayuwar duniya) kawai wannan ɗaukaka ta mutumtaka ɗin ma ba komai bace.
Za mu iya gane haka ta hanyar misalai guda biyu:
Kuɗi da kuma abinda kuɗm zai iya saye (kaya). Wani lokaci darajar kayan kansa kuɗi da yawa, ba wai abinda aka sarrafa ƙayan da shi ba domin abubuwan da aka haɗa kayan da su ne ɗai-ɗai sai kaga ba su yi rabin ƙudin ƙayan ba. A wasu lokuta kuma, fasaha da shaharar wanda ya sarrafa (kera) ita kayan, shi ke sa a sayi kayan da daraja.
To haka ma ɗan adam yake, halitta (kaya) ne na Allah. Allah tsarkakakke da ɗaukaka, cikin ikonsa, ya halicci sammai da kassai, yadda kai da ka duba ka san akwai wanda ya yi su.
To har idan hasken’ Imani ya shigi mutum, komai (na game da halittar Allah) zai iya gane shi. A matsayin na mai imani kuma, zai iya sa wasu ma su gane hakan, kai har dai mutum shi a ƙashin kansa ya kai ga faɗin. “Ni fa halitta ne na Allah maɗaukaki. “Ni cikin rahamarsa na ke rayuwa.” Wannan shi ne Imani, wanda ke danganta abin halitta da mahalicci. Kamar mutum na tattare ne ta wurin la’akari da wanda ya samar da shi. Kenan mutum mai girman mai daraja (mai Imani kenan) kan zama wanda Allah ke kula da shi, kuma ya zama baƙon Allah, wanda ya cancanci ya zauna a aljanna fiye da duƙƙan sauran halittu.
Amma kuma, kafirci, wanda yake shi ne gurɓacewar dangantakar ɗan adam da mahaliccinsa, idan har ya shigi mutum, to (shi mutum din) ba zai iya gane komai ba (na cewa Allah ne ya samar da halitta) zai kasance cikin duhu. Saboda kuwa, idan har aka manta da mahalicci, tunanin ma wa ya yi halitta, ba zai taso ba, sai dai akasin haka, wato cewa, komai samamme nc, ba wanda ya samar-da shi. Duk waɗannan kyawawan halittu (na Allah) basa iya sanin wa ya samar-da su, sai dai kawai su riƙa ɗaukar cewa samammu ne da ma can; saboda irin wannan tunani, sai ka ga (a idon waɗannan mutane) komai ya rasa ƙimar da ta dace da shi. Kai ko da (abubuwan halitta) sun kai ƙyalƙyalin zinari da zabardaji, sai su yi duhu a idon waɗannan mutane. Kira da darajar irin waɗannan mutane ta tsaya ne kawai a matsayin su na mutane, shi ke nan!
Kuma kamar yadda muka faɗa (a baya manufar kasancewar ɗan adam mutum, shi ne ya rayu na ɗan wani lokaci, yana mai rauni, mabukaci cike da takaici. Sannan ya mutu, ya ruɓe, ya zama kasa. Ɗon Allah, dubi yadda kafirci ke bata rayuwar mutum, ya maida daga mai daraja, mai kima, zuwa mara daraja mara kuma kima.
Hujja Ta Biyu
Kamar yadda Imani yake haske, wanda ke haskawa mutum, ya kuma sa mutum ɗin ya fahimta.
Haka kuma imani ke haskakawa ɗan adam duniya, ya gane abinda ya wuce da abinda zai zo. Zan yi bayanin wannan Magana ta danganta mafarkin da wannan aya:
Allah shi ne majiɓincin waɗanda suka yi imani; yana fitar da su daga cikin duhu ya kai su ga haske.
Kur’ani.2:257
Ga Mafarkin:
Na yi mafarkin ga ni a kan wata gaɗa da aka gina a tsakanin wasu tsaunuka guda biya, waɗanda suke daura da juna. Karkashin gaɗar nan akwai wani kwari, mai tsananin zurfi. Ni kuma gani a kan gadan nan. Wani matsanacin duhu duk ya kewaye duniya. Dana duba dama na sai na ga wani katon rami mai tsananin duhu, na kuma duba hagu na naga gagarumin haɗari, ga kuma tsabar duhu. Na kuma duba ƙarƙashin gadar, na ga rami, wanda zurfinsa ba iyaka. Ina da wata tocila a hannuna mara haske. Idan na haska ina gani kaɗan. Sai na ga wasu abubuwan ban tsoro. Sai na ga dodanni da zakoki sun kewaye ni. Nan da nan sai na ce: “Kai tocilan nan ma dai bata hasƙaƙa mani komai.” Sai na wurgar da ita ƙasa na bi zan take. Takawar da zan yi sai na ga wuri ya yi haske, kai ka ce an kunna wata ƙatuwar fitila, ko’ina ya yi haske. Nan da nan komai ya koma kamanninsa.
Sai na ga gadar da nake kai ashe wani shararren titi ne, katon rami da na gani a dama na, ashe wani lambu ne cike da bayi ma su bautar Allah. A haguna kuma wanda nake ganin abubuwan ban tsaro, ashe wani wurin shaƙatawa ne da jin daɗi dake bayan wani tsauni. Doɗannin nan kuma da na gani masu ban tsoro ashe dabbobi ne da na saba da su, irin su raƙumma, ɓauna, tumaki da awaki. Sai na ce: “Dukkan yabo ya tabbata ga Allah saboda hasken Imani” (da ya ba ni). Kuma na karanta wannan aya:
“Allah shi ne majiɓincin waɗanda suka yi imani, yana fitar dasu daga cikin duhu, ya kaisu zuwa ga haske.”
Sai na farka daga barcina.
Wannan na nuna cewa: tsaunukan nan guda biyu, na nuna farkon rayuwa da kuma karshenta, da kuma abinda zai biyo baya. Gadar kuma da na gani, har wa yau rayuwa ce, damana kuma shi ne abinda ya wuce (na rayuwa); ya yin da a haguna kuma abinda zai zo ne (na rayuwa). Tocilan nan kuma itace halayyar ɗan adam. Dodannin kuma su ne yanayin rayuwar duniya da abin da ya tattaru gare ta.
Ta haka, wanda ya bi son ransa a cikin rayuwa, ba zai haɗu da komai ba, face abin nan da na fara gani a cikin mafarkina, wanda ke nuna kabari mai zurfi mai cike da duhu. Ya yin da rayuwa ta nan gaba ke cike ko ke nuna tasowar haɗari da kuma faruwar wasu abubuwa. Wannan ya yi ɗaiɗai da ayar dake cewa:
“Waɗanda suka kafirta kuma majibantarsu su ne ɗagutai; suna fita daga cikin haske suna kai su cikin duhu.”
Kur’ani 2:257
Amma idan irin waɗannan mutane, suka samu shiryuwa, Imani ya shiga zukatan su, suka kuma yarda da littafin Allah, to sai su haɗu da ɗaya ɓangare na mafarkina (bayan da na fasa tocila). Duniya ta haska musu kamar yadda aya ke cewa:
“Allah shi ne hasken sammai da kasai.” Kur’ani 24:35
Daga nan mutum zai gane a cikin ƙoƙon zuciyarsa wurin nan da aka gani kamar katon rami, ba fa katon rami ba ne, wuri ne da tsarkakan bayin Allah a kowane bayan tsawon lokaci (ƙarni), idan sun gama bautar Allah a ƙarƙashin jagorancin wani annabi ko wani aliyi, sai su riƙa fadin: “Allah shi ne mafi girma.” (Allahu Akbar) daga nan sai su koma wani wuri maɗaukaki. Har wayau wurin da naga kamar ana walima, wuri ne (ko kuma fada ce) wanda mai rahama ya, shirya a cikin gidan aljanna, wanda (bayin Allah na ƙwarai) ke samu bayan mutuwa. Daga nan mutum zai fahimci cewa, haɗari da girgizar ƙasa da ya auku a cikin mafarkin nan ba komai ba ne face kamar dai mika wuya ne, wanda yake kamar abu ne mai wuya, amma mai sauƙi ne kamar ruwan marmaro. Daga nan sai mutum ya gane cewa mutuwa, kamar matakin farko ne ga, rayuwa maɗauwamiya, kuma kabari kofa ce zuwa ga jin daɗin da ba shi a da karshe. Ƙai kanka za ka iya ganc haka, kwatanta wannan misali a cikin zahiri ka gani.
Hujja Ta Uku
Imani, haske ne kuma ƙarfi ne, ba shakka, wanda yake da ƙwaƙƙwaran imani, to zai iya ja da duk duniya, kuma ya jure wa duk wani matsi gwargwadon imaninsa. Yana faɗin cewa: “Na dogara ga Allah to haka, zai ta gudanar da rayuwarsa babu abunda zai same shi. Duk wanda ya miƙa komai zuwa ga Allah mai cikakken iko, haka zai ta tafiya cikin rayuwa a cikin sauƙi har ya gama da rayuwa matabbaciya, daga nan sai aljanna, domin jin daɗin na din din din. Amma ga wanda bai wakkala komai zuwa ga Allah ba, maimakon rayuwa mai sauƙi sai ya faɗa cikin wahala, ya koma mafi ƙasƙantar maƙasƙanta. Muna iya cewa imani, shi ke haifar da kaɗaita Allah, kaɗaita Allah kuma, shi ke haifar da miƙa wuya ga Allah, miƙa wuya kuma shi ke haifar da dogaro ga Allah wanda shi kuma, shi ke haifar da rabauta a lahira.
Abin lura shi ne ba wai daga mutum ya dogara ga Allah, shi ƙe nan, ba wani abin da zai same shi, a’a akwai abubuwa da za su same shi; sai dai kuma duk abinda zai same shi, to fa daga Allah ne, kuma akwai magani nsu. Sanin cewa komai daga Allah ne, wani ƙwaƙƙwaran nau’ine na ibada. Mutum kuma ya san cewa sakamako ne daga Allah, ya kuma miƙa godiya gare shi.
Wanda ya dogara ga Allah, da wanda bai dogara ba, ƙwataantasu cikin wannan labari ka gani:
A wani zamani (da ya wuce) waɗansu mutane biyu ɗauke da kaya, suka shiga jirgin ruwa shigarsu ke dawuya sai ɗayan ya sauke kayansa ya hau kai ya zauna, ɗayan kuwa sai ya tsaya da kaya a kai saboda da ma shi sakarai ne, mai ji-ji da kai.
Ganin haka, sai gudan ya ce masa: “Sauke kayan mana, ka huta.”
Sai ya ce: “a’a, ina gudun kada su ɓace ya ci gaba da cewa: “haba ga ni dai da karfina, mene ne, kuma sai na sauke?
“Sai abokin tafiyarsa ya ce masa: “Kada ka ji komai, ƙayan ka ba za su ɓace cikin wannan jirgi ba. Kada ka yi shakka game da shi wannan jirgi, zai iya ɗaukar mu ya da kayan mu. Kai dai ka saukc kada jiri ya debe ka, ka faɗa ruwa; ko ma ba haka ba, sannu-sannu za ka fara jin nauyin wannan kaya. Kai! Bar ta wannan ma, idan shugaban jirgi ya ganka, da kaya a ka, to ɗauka zai yi kai mahaukaci ne, ko kuma ya ɗauka ka raina masa jirgi ne, kana ganin jirgin shi bai iya ɗaukar ka, kai da kayanka, saboda haka, sai ya sa a sauke ka, ko kuma ya sa a kulle ka. Kai duk ture waɗannan dalilai ma, kai kanka ai ƙasƙantar da kanka kake, a idon mutane, saboda abinda kake nuna musu shi ne, rauni da kasawa, duhun kai da alfaharin ƙarya, wanda ya maida kai sakarai abin dariya a idon mutane. Daga nan sai shi wannan mai ɗauke da ƙaya ya fahimci manufar zancen abokin tafiyarsa, saboda haka sai ya sauke kayan, ya ce: “Kai Allah dai ya saka maka da alheri, ka ga yanzu na huta da wahala, da kuma dariyar jama’a.”
Saboda haka, ya kai mutum, wanda bai yarda da Allah ba, kai ma ka farka ka komo cikin hankalinka, ka mika wuya ga Allah, ko ka samu kuɓuta a idon duniya, ya kasance ka daina samun faɗuwar gaba ya kasance ba ka zama wawa ba a idon duniya, ba ka haɗu da takaici ba a lahira da dai sauransu.
Hujja Ta Huɗu
Haƙiƙa imani kan cika halittar mutum, yakan kuma maida mutum ya zama sarki. Tunda ko haka ne, babban aiki ga mutum shi ne ya yi imani, ya kuma mika wuya, don kuwa kafirci kan maida mutum cikaƙƙen dabba.
Akwai dubban hujjoji da za su tabbatar da wannan Magana; ɗaya daga cikinsu ita ce samar da halittar mutum da dabba a wannan duniya. Bambancin halittu biyun shi ne imani. Mutum ya samu matsayinsa na mutumtaka ne ta hanyar imani. Ita dabba kan zo duniya ne tare da fahimtar wasu abubuwa, kuma cikin ɗan lokaci kaɗan sai ka ga ta fahimci komai da komai. Ɗauki misali ga mashinllera (wato tsettsewala) Wata tsuntsuwa ce da kuma kudan zuma waɗanda cikin ƙwana ashirin da zuwansu duniya, sai kaga sun fahimci komai amma mutum sai bayan ya shafe shekaru ashirn sannan ne zai fara fahimtar abubuwa.
Wannan na nuna cewa dabbobi (ba kamar mutum ba) ba wai ƙwarewa suke ba (ga ayyukansu) ta hanyar zuwa neman ilmi kamar yadda ɗan adam yake yi, sai dai su (dabbobin sukan samu hakan dadai da ƙwazonsu da iyawarsu). Saboda haka su dabbobi basa saɓawa Allah, komai suka yi bauta ce. Wannan ya sa su rayuwarsu ita ce bauta a ko yaushe.
Mutum shi ne ya kamata a ce ya san komai da komai da zuwansa duniya, amma bahaka yake ba! Saboda rauninsa da yanayin halittarsa, bai gama fahimtar komai a cikin shekaru ashirin da haihuwarsa. Ya zame masa dole, ya ci gaba da ƙoyon abubuwa har zuwa ranar da zai koma ga mai duka (Allah). Kai saboda raunin ilmi na mutum, bai fara bambance mummuna da kyakkyawa ba sai ya shekara goma sha biyar (15), daga nan ne (saboda yanayi da baiwa da Allah ya yi wa ɗan adam), sai kaga ya fara gane ko fahimtar abubuwa dake da amfani a gare shi.
Saboda haka, babban aikin mutum shi ne neman ilmi, da sanin yadda zai bautawa Allah, tare da miƙa wuya a gare shi. Ma’ana mutum ya tambayi kansa: “Cikin rahamar Allah waye ke gudanar da rayuwata haka’.’ Alheri da baiwa da na samu har na kawo wannan lokaci, wane ne ya yi mani su? ‘Waye ya raine ni, tun ina cikin rauni, har na kawo wannan lokaci?”
Dole ne mutum ya san wa ya halicce shi ya kuma samar masa da waɗannan abubuwa, ya kuma miƙa wuya a gare shi, a cikin halin rauni ko cikin halin rashi; dole mutum ya fuskanci Allah da buƙatunsa. Kuraa (ya yi ƙoƙari) ya kai ƙololuwar bautar Allah a halin rauni da kuma talauci.
Mutum zai samu kama ta ne kawai ta hanyar sani da kuma miƙa wuya ga Allah. Mutum dangane da halittarsa da kuma abinda yake iya yi a komai nasa, ya dogara ne a kan ilmi. Haka ma tushensa da kuma tsatsonsa, da ficensa ya dogara nc ga Allah, wanda wannan shi ma zai samu ne kawai ta imani da Allah.
Daɗin ɗaɗawa, tun da dai mutum, a kowane hali, kuma a kowane yanayi cikin jarabawa yakc daga fannonin rayuwa dabam daban ga rauni ga kuma bukatu nasa na yau da kullum, to bayan imani da ya yi sai kuma ya miƙa wuya ga Allah. Mika wuya, shi nc ainihin tushen bautar Allah. Dubi misaliqn yaro, idan yana buƙatar wani abu, yalcan yi kuka ne a ba shi, wani lokaci kuma ya tambaya, ma’ana, yakan yi nuni ko kuma ya yi Magana, sai kaga an biya masa buƙatarsa. Haka shi ma mutum a gaban Allah mai rahama mal jin kai, yakan yi kuka ne ga Allah ko kuma ya roki Allah ga abin da yake bukata, sai kaga (Allah) ya ba biya masa buƙatarsa. Amma kuma idan daga bayan ya samu ya fara tunanin cewa:
“Mene ne na damun kai, abinda bai kai in tayar da hankali ba, na zo ina tada hankalina, wannan abu dai, ko ta halin ƙaƙa zan samu, gani da dabaru kamar me?” ya dai nuna rashin godiya da tawali’u ga Allah, ta haka sai ka ga ya haɗu da matsananciyar azaba. Allah kiyashemu, amin.
Hujja Ta Biyar
Imani yakan tilasta yin addu’a ga Allah, don samun biyan buƙatu daga Allah, don samun dama wani yanayi ne na ɗan adam; har Allah ya ce.
“Ka ce: Ubangijina ba zai damu da ku ba, ba don addu’o inku ba.”
Ƙur’ani 25:77
Ma’ana: Wace daraja za ku samu idan ba ku yin addu’a ga Allah? Wato ba ku rokon Allah. Allah ya yi umarni da ccwa:
“Ƙu roƙe ni, zan karba maku.” Ƙur’ani 40:60
Idan ka ce: “Ƙo yaushc sai addu’a nake yi, amma shiru kake ji. Ayar Ƙur’ani ta ce ana amsar kowace addu’a.”
Amsar ita ce: Amsar addu’a da biyan buƙata wasu abubuwa ne mabambanta. Ƙowace addu’a ana amsa ta, amma biyan buƙatar abinda aka roƙa ya dogara ne ga hikimar Allah maɗaukaki. Misali: Idan yaro mara lafiya zai ta kira: Likita likita!!” Idan likitan ya amsa ya tambaye shi: “Me kake so?” Yaron ya amsa: “ba ni wancan maganin” Likitan zai ba shi maganin da ya tambaya, ko kuma zai dauƙo wani wanda ya ga ya fi dacewa ya ba shi. Idan kuma ya ga cewa rashin lafiyar yaron ba ta buƙatar magani, to sai ya kyalc shi.
Haka yake ga Allah masanin Gaibu (ɓoye). Yana karbar duƙƙan addu’a ta bayinsa. Allah cikin rahamarsa da iyawarsa, yakan mayar da babu zuwa ga akwai ta hanyar ɗa ya so, ba ta hanyar da mutum ke so ba. Allah ta cikin hikimarsa, yakan ba da abinda aka roka, ko kuma ya ba da fiye da abinda aka roka, ko kuma, da yake shi ne ya san daidai, sai ya jinkirtar.
Haka nan addu’a, wata nau’I ce ta bauta, wanda sakamakonsa sai a lahira. Kowace addu’a tana da lokaci da kuma dalilin yinta. Misali: akwai salloli da addu’o’i da ake yi a lokacin fari, don samun ruwa. Akan yi su ne don bauta ga Allah, da kuma neman biyan buƙata. Idan aka yi su don samun ruwan kawai to ba za su samu karbuwa ga Allah ba, haka kuma kusufin rana da wata lokuta ne da ake sallolin kisfewar rana da wata. Waɗannan salloli ba wai ana yinsu ba ne don kawai rana da wata su fito, a’a, ana yin su ne domin bautar Allah.
To haka ma sallar sha-da-fari, haka kuma addu’o’in da ake yi don yayewar wasu jarrabu da masifu, lokacinda mutum ke gane rauni da kasawarsa, sai ya yi addu’a da neman tsari ga Allah wanda ya mallaki dukkan (kuma ciƙaƙƙen) ƙarfi.
To kuma ko da ba’a ga biyan buƙata wa ba (bayan da aka yi addu’a) ba za’a cc ba’a amsa addu’ar ba, sai dai a ce, ai har yanzu akwai lokaci, Allah shi ne cikin rahamarsa da jin ƙansa, zai yaye.
Kenan dai ashe, addu’a ba wai neman yayewa ba ne kawai, a’a wani nau’i ne ma na bauta.
Haka kuma abinda yake a zahiri kamar yadda ayoyin ƙur’ani suka nuna. Shi ne cewa kamar yadda kowace abin halitta take bauta da-tsarkake Allah, haka kuma yake rokon (yin addu’a ga Allah.) Sukan yi haka ta hanyar da Allah ya hore musu, (kamar tsirrai da dabbobi) ko kuma ta baka (kamar mutane da aljannu) halittu sukan yi addu’o’i su roki abinda bai yiwuwa su samu sai ta hanyar rokon Allah, Ubangijin kowa da komai. Ƙowane abu mai rai yakan tsinci kanshi wani lokaci cikin ƙaƙa ni-ƙayi ko kuma neman kaucewa wani abu, ta haka sai ka ga yana neman tsari daga wurin Ubangiji mai Rahama.
Ya istidat lisanıyladır. Bütün nebatatın duaları gibi ki her biri lisan-ı istidadıyla Feyyaz-ı Mutlak’tan bir suret talep ediyorlar ve esmasına bir mazhariyet-i münkeşife istiyorlar.
Veya ihtiyac-ı fıtrî lisanıyladır. Bütün zîhayatın, iktidarları dâhilinde olmayan hâcat-ı zaruriyeleri için dualarıdır ki her birisi o ihtiyac-ı fıtrî lisanıyla Cevvad-ı Mutlak’tan idame-i hayatları için bir nevi rızık hükmünde bazı metalibi istiyorlar.
Veya lisan-ı ıztırarıyla bir duadır ki muztar kalan her bir zîruh; kat’î bir iltica ile dua eder, bir hâmi-i meçhulüne iltica eder, belki Rabb-i Rahîm’ine teveccüh eder. Bu üç nevi dua, bir mani olmazsa daima makbuldür.
Dördüncü nevi ki, en meşhurudur, bizim duamızdır. Bu da iki kısımdır: Biri, fiilî ve halî; diğeri, kalbî ve kālîdir. Mesela, esbaba teşebbüs, bir dua-yı fiilîdir. Esbabın içtimaı, müsebbebi icad etmek için değil, belki lisan-ı hal ile müsebbebi Cenab-ı Hak’tan istemek için bir vaziyet-i marziye almaktır. Hattâ çift sürmek hazine-i rahmet kapısını çalmaktır. Bu nevi dua-yı fiilî, Cevvad-ı Mutlak’ın isim ve unvanına müteveccih olduğundan kabule mazhariyeti ekseriyet-i mutlakadır.
Wata addu’ar kuma ita ce wadda muke yi, mu mutane. Wani lokaci, mukan roki Allah da bakinmu da kuma zuciyoyinmu. Mukan yi waɗannan addu’o’i ne domin samun wasu abubuwa da mu kanmu ba za mu iya samu ba. Abin faranta rai mai yin addu’ar ya san akwai mai sauraron sa, ya yi imani da cewa lallai akwai wanda ya san abinda ke cikin zuciyarsa, wanda zai iya biya” masa kowace irin buƙata tasa. Irin wannan addu’a takan samu karbuwa a mafi yawan lokuta, tunda dai ana yinta ne kai tsaye, zuwa ga mai kyauta mai Rahama, Mafi tausayin bayinsa, mai kawar musu da dukkan rashi.
Saboda haka, ya kai mutum mabukaci, kada ka yi watsi da yin addu’a wadda ita ce hanyar kaiwa ga taskokin rahama da kuma karfin da ba ya ƙarewa. Miƙe tsaye, ka rike shi ƙwarai, ko ka samu kaiwa ga kololuwar ɗaukaka ta’yan adam. Rika sa kowa da kowa a cikin addu’arka. Rika cewa “Gare ka kawai, muke neman taimako” (ba gare ka kawai nake neman taimako ba); ka kasance mafi kyaun abin kwatance na halitta.
BABI NA BIYU
MAGANGANU BIYARDA SUKA SHAFI RASHI DA SAMU NA MUTUM:
(Shi mutum an halicce shi ne cikin kyakkyawan tsari, aka kuma ba shi ikon fahimtar abubuwa, to ke nan an sa shi cikin fagen jarrabawa, inda ko dai ya kai ga ɗaukaka. Ko kuma ga kaskanci, da sauransu. An turo shi wannan duniya ne domin ya zama wata aya ta maɗaukaki mai Rahama, kuma haka Allah ya aza shi a hanyoyi biyu waɗanda za su kai shi ga ɗaukaka ko kaskanta. Za mu yi bayanin wannan gaibu a cikin maganganu biyar.)
MAGANA TA FARKO
Ɗan adam yana wani matsayi na buƙatar komai na duniyar nan wanda ke da ɗangantaka da shi. Bukatun mutum ba su da iyaka. Yadda yake son rani haka yake soo damina. Yadda yake son mazauni, haka yake buƙatar aljanna maɗauwamiya. Haka kuma yadda yake son ganin wani aboki nasa, haka, yake son ganin Allah maɗaukaki mai rahama, kuma kamar yadda yake son ziyartar wani masoyi (nasa) haka yake so Allah ya biya nasa bukatunsa, domin saduwa da abokansa da ya rasa; haka kuma akwai buƙatar mutum ya nemi tsaro ga mai maɗaukakin karfi. Saboda kuwa shi ne mai jinkintarwa a duniya, sai a lahira ya ba da, wannan yana daga cikin abubuwan ban mamaki nasa, kawar da wannan duniya, ya maye ta da ta lahira.
Saboda haka ga mutum dake wannan matsayi abin bauta na gaskiya kawai shi ne Allah, wanda a hannunshi taskar komai take, wanda kuma babu wani abu mai ɓoyuwa a gare shi, ya gane ko ina da saninsa, shi baya buƙatar wurin zama, ya baranta daga dukkan rauni, babu kasawa ko nakasa a gare shi. shine Mai tabbataccen karfi, Maɗauƙaƙi Mai Rahama, kuma Shi ne Mai hikima.
Saboda haka ya kai mutum, idan kai bawa ne na Allah to za ka samu babban matsayi fiye da sauran halittu. Amma idan ka kauce, ka daina bautarsa, ka kama bautar waninsa, to ka zama bawan raununan halitta. Haka kuma idan ka bi son ranka, ka yi watsi da dogaro ga Allah da kuma rokonsa ka shiga alfahari da cika baki, to sai ka ƙasƙanta ka koma kasa fiye da yadda kiyashi ko kuɗan zuma idan an ƙwatanta su da sauran halittu, sai ka fi kuda ko gizo-gizo rauni. Haka kuma sai ka fi komai na duniya sharri da cutarwa. AUah ya tsare mu, amin.
Haƙiƙa, ya kai mutum kana da fusƙoƙi guda biyu: fuska ta farko ita ce matsayinka na abin halitta, akwai ka da sanin abu mai kyau, da kuma ɗaukan matakin da ya dace, da kuma bin hanyar gaskiya. Fuska ta biyu kuma ita ce ta ɓarna, da ko-in-kula, da mugunta da kuma son-rai.
Idan muka ɗauki fuska ta farko, za mu ga cewa akwai ka da rauni, idan ko muka dubi fuska ta biyu za mu ga cewa, ka kere ƙasa da tsauni, kai har ma da samaniya, ka ɗaukar wa kanka kayan da ya fi nasu. Duba Kur’ani 33:72 me yasa haka?
Dalili kuwa shi nc, a duk lokacinda ka aikata wani aiki ƙyaƙƙyawa ka yi shi ne ko kuma ka aikata shi ne gwargwadon karfinya da iyawar ka. Amma a duk lokacin da ka aikata wani mummunan aiki to muninsa da ɓarnarsa watsuwa suke sai illa-masha Allah.
Kafirci cuta ce kuma barna ce, kuma musuntawa ce ga samuwar Allah. Wannan mugun abu (kafirci) ƙaskantuwa ne ga halittun duniya gaba ɗaya, tozarci ne ga sunaycn Allah (mai girma) kuma cin zarafin ɗaukacin bil-adama ne. Saboda kuwa su sun kai wani matsayi na ɗaukaka. Amma kafirci ya musunta haka, ya maida su wasu abubuwan wasa waɗanda (wai) suke samammu tun fil- azal. Ya maida halittun Allah wani matsayi na cewa idan sun mutu, sai su ruɓe, shi kenan! Yin haka tozarci ne ga siffofin Allah da halittunsa waɗanda ya samar kuma ake iya gani. Kafirci yakan sa mutum ya zama raunanne, abin tausayi, maƙaskancin makaskanta, a cikin “yan adam. Saboda me, saboda kuwa mutum a matsayinsa na kalifar Allah a bayan ƙasa wata alama ce dake bayyana siffofin Allah wanda Allah cikin hikimarsa ya ɗaukaka zuwa wani matsayi maɗaukaki, wanda ya haye kasa kanta, ya kuma fi duk wani tsauni tsawo, har ya kai ga samun ɗaukaka fiye da mala’iku, Kafirci, yakan maida mutum wata halitta, mara amfani.
A takaice dai: Mutum wanda zuciyarsa ta yi kanta da barna da mugunta, zai iya aikata ɓarna wadda ba ta da iyaka. Saboda zuciyarsa ta riga ta dushc da barna. Zai iya aikata komai na barna, amma ya kasa aikata kaɗan na ƙyaƙƙyawa. Misali: a cikin rana guda, zai iya kada gini, amma ba zai iya tada wannan gini ba a rana guda. Amma idan mutum ya kauce wa son ransa, ya kuma nemi shiriyar Allah da gafararsa, to Allah zai shiryar da shi, kuma ya gafarta masa zunubbansa. Allah ya ce:
“Waɗanda suka tuba, suka kuma yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, to Allah zai juya munanan ayyukansu zuwa ƙyaƙƙyawa.”
Kur’ani 25:70.
Mummunan aikin nan nasa mara iyaka, Allah zai juya shi zuwa ga kyakkyawan aiki wanda ba shi da iyaka. Zai kai ga ya samu matsayi na ɗaukaka.
Saboda haka ya kai ɗan- adam mara kula, dubi irin yadda ni’ima da ƙyautar Allah take. Da ya so sai ya ninka aikin saɓo guda ɗaya ya koma dubu; aikin lada kuma {komai yawan shi} ya ba shi lada ɗaya, ko ma ya hana inya so, kuma babu wanda ya isa ya ce bai yi daidai ba. Amma Allah bai yi haka ba; mummunan aiki sai ya ba shi zunubi ɗaya ƙyaƙƙyawa kuma lada goma in ya so sai ya ba shi lada sabain, ko kuma ɗari bakwai, ko dubu saba’in ko ma fiye. Daga wannan Magana za mu iya fahimtar cewa idan Allah ya sa mutum wuta, to ya yi masa adalci, idan ko ya sa mutum aljanna, to ya dai rufe shi ne kawai da ni’marsa.
MAGANA TA BIYU
Ɗan Adam fuskoki biyu gare shi. Fuska ta farko, ita ce ta son rai. Wadda da ita ya ke kallon ƙawace-ƙawace na duniya. Fuska ta biyu ita ce ta bautar Allah, ya ke kuma tuna abinda zai samu a lahira.
To idan muka dubi mutum ta fuskarsa ta farko, za mu ga cewa mutum dai kusan halakakke ne saboda waɗannan dalilai: baya iya yi wa kansa komai sai abinda aka yi masa, ga shi cikin ‘yar rayuwa gajera, wata rana a neme shi ba shi gangan jikin ma bata; shi da sauran halittu haka za su waste a bayan kasa.
Idan kuwa muka duba fuska ta biyu ta ɗan adam, za mu ga cewa duk da rauninsa da kasawarsa, Allah ya ɗaukaka kuma ya daraja ta mutum. Saboda shi Allah maɗaukaƙi shi ne ya halicci mutum da rauni da kasawa, saboda mutum ya san akwai fa wanda yake da iko da shi. Mutum ya san fa akwai mai tabbacin karfi mai Rahama, wanda karfinshi da ikonshi da ƙyautar Shi ba su da iyaka.
Mutum kamar wani tsiro ne. wannan tsiro ya yadu da yardan Allah, tun daga ƙarƙashin kasa har ya kai ga ya fito wannan duniya shi ma (tsiron) rokon Allah yake Allah yasa ya girma ya kai ga ya zama bishiya.
Amma idan har bai samu kyakkyawan yanayi ba, to sai ka ga ya lalace, har ya kai ga ruɓewa.
Amma har tsiron ya samu kyakkyawan yanayi kamar yadda Allah ke cewa:
‘fo zai kasance shi (tsiron) ya watsu har ya kai ga ya zama babbar bishiya wadda za’arika ƙaruwa da ita.
To, kamar haka ne Allah ke tsara rayuwar ɗan Adam. Idan mutum ya samu yanayin rayuwa mai ƙyau to za’a ga rayuwarshi ta ƙyautata.
Amma idan ɗan adam ya samu akasin yanayin rayuwa mai ƙyau, sai ya lalace ya ruɓe, kamar wancan tsiro da bai samu wuri mai ƙyau ba.
Amma idan mutum ya reni rayuwarsa da ruwa na Musulunci da haske na imani ta hanyar bautar Allah kamar yadda ya yi umarni a Kur’an, kuma ya yi aiki kamar yadda ya dace, to zai kasance abin misali abin koyi a wannan duniya kuma a lahira ya samu babban rabo, kuma Allah ya azurta shi da zuri’a ta gari. Kamata ya yi mutum ya mayar da tunaninsa da ma komai nasa, zuwa ga abinda zai samu na har abada a rayuwarsa ta lahira.
Ci gaba, kamar yadda mutane suka ɗauka, ba shi ba ne ƙoƙarin samun jin dadin rayuwar duniya ta kowace hanya ta hanyar cuta, da maguɗi da yaudara da ɗai duk wasu dabaru da basu dace ba, wannan ba ci gaba ba ne - koma baya ne. Haƙiƙa na ga wannan wata rana a cikin mafarki.
Wai wata rana ne zan shiga wani babban gari, sai na ga wani babban wuri. A gaban wannan wuri ana ta biki, kusan hankalin kowa ya koma wajen bukin. Sai na duba, sai na ga shugaban wannan wuri, yana tsaye a wata kofa yana wasa da kare. Ga mata nan kuma ko ina tare da samari ana tattaunawa; ya yin da manyan mata kuma ke ta dawainiyar daidaita yara. Mai kula da shigi da fice kuma, yana kan aikinsa. Sai na lura na ga cewa can cikin wannan wuri, ba komai. Ba abinda ke faruwa a ciki, abinda ya kamata a yi a cikin ne ake yi a bakin ƙofar wannan wuri. Kai da ganin mutanen wannan wuri ka san abinda ake kira ɗa’a ya yi musu kaɗan, shi yasa suke lalacewa a wannan wuri.
Sai na wuce wannan wuri, har na kai wani babban wurin kuma. Na ga wasu manyan karnuka suna tsaron kofa. Wurin nan dai ga shi nan ne kawai. Da na duba ciki sai na ga mai ban sha’awa wurin ne. mutanen ciki, kowa sai kula da aikinsa yakc yi. Mazaje na kula da yadda komai ke tafiya. Can gefe kuma ga mata na koyar da yara ƙanuna. Manyan mata kuma, sai ƙara ƙawata wajen suke. Can sama kuma ga shugaban wurin yana tattaunawa da manyan mutane. Tunda su ba su kula da ni ba, sai na yi ta yawo ina ba idona abinci.
Daga nan sai na bar wurin, na zo na tambayi labarin waɗannan wurare. Sai aka ce mani, wancan wuri na farko inda ga mutane waje amma ciki fanko, wuri ne na kafirai tsantsa. Amma wuri na biyu inda na ga mutane a kintse cikin natsuwa, wuri ne na Musulmi tsantsa. Sai kuma na iso wani wurin. sai naga an rubuta suna a wani katon gida ko in cc fada kamar haka: (SAID). Ba sai na ruɗe na duba, na duba. na sake dubawa, kai sai da ta kai kamar ina ganin kaina a ciki sai kawai na farka.
Bari in baku fassarar wannan mafarki nawa; Allah ya sa ku fahimta.
Wannan wuri, wato gari, kwatakwacin rayuwa ce kanta. Waɗannan wurare, biyu kamar mutane ne biyu dukkan su kowa Allah ya hore masa ji da gani da tunani. Kowa na ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa uku wato ji da gani da tunani yana da rawar da yake takawa na bauta ko fanɗarewa. Waɗannan karnuka da mai tsaron kofa, kamar zuciya mutum ne. to mutum ya bari ita zuciya ta rinjayi waɗancan abubuwa uku, hakan ba karamin ci baya ba nc. Idan ko har zuciyarsaza ta kula da aikinta, kamar yadda karnukan biyu suka kula da aikinsu to komai zai tatl cikin tsari. wato gani da ji har ma da tunani, to za su yi aikinsu cikin tsari kenan. Idan ko ba haka ba, to na bar maka sanin sauran.
ÜÇÜNCÜ NÜKTE
Da za ka kalli mutum, sai ka ga ccwa halitta ce mai rauni, kasasshiya ta wurin aikace aikace (sai dai taimakon Allah). Abinda shi kansa zai iya yi idan da za’a bar shi, sai ka ga abu ne da bai taka kara ya karya ba.
Kai dabbobin gida waɗanda aka hore wa mutum idan da za ka ƙwatanta su da ɗanginsu na daji, sai kaga na gida sun gaji dabi’u na mai gidansu, wato dabi’u ua rauni da kasawa.
Fakat o insan, infial ve kabul ve dua ve sual cihetinde, şu dünya hanında aziz bir yolcudur. Ve öyle bir Kerîm’e misafir olmuş ki nihayetsiz rahmet hazinelerini ona açmış. Ve hadsiz bedî’ masnuatını ve hizmetkârlarını ona musahhar etmiş. Ve o misafirin tenezzühüne ve temaşasına ve istifadesine öyle büyük bir daire açıp müheyya etmiştir ki o dairenin nısf-ı kutru –yani merkezden muhit hattına kadar– gözün kestiği miktar, belki hayalin gittiği yere kadar geniştir ve uzundur.
Amma idan har mutum ya fahimci cewa shi fa ba komai ba ne a wannan duniya na mai Rahama, kuma yana jin daɗi ne saboda ƙyautar da ya yi masa, to zai ji daɗi nan, kuma can ma kiyama yana da hutu da matsayi na ɗaukaka.
Ƙari a ƙan kari shi nc, gaɓan mutum waɗanda za su ba da shaida a kan sa ranar ƙiyama, za su yi hakan ta hanyar bada kyakkyawar shai da game da shi duka gaɓoɓin da Ubangiji ya yi wa mutum, ba ya yi su ba ne su zama na amfanin wani ɗan lokaci, ya yi su ne su zama na amfanin din-din-din.
Idan har za ka kwatanta irin baiwar da Allah Ubangiji ya yi wa ɗan adam ta wurin halitta da kuma wadda ya yi wa dabbobi, za ka ga cewa ɗan adam ya tsere wa dabbobi nesa ba kusa ba. Amma ta wajen jin daɗi da more ƙirar da Allah ya yi wa kowanensu, sai aga dabbobi sun fi ɗan adam jin dadi da more ƙirar da Allah ya yi wa kowannensu. Saboda me?
Saboda shi ɗan adam akwai dokoki da ke jagorancin rayuwarsa. Akwai abin da zai tuna wanda ya wuce ya yi nadamarsa, akwai kuma abinda zai tuna wanda zai zo, ya shiga halin zan yi. Saboda haka idan ya wuce gona da iri ga yadda yake tafiyar da gaɓoɓinsa, to sai ya yi da-na- sani!
Dabba fa? Dabba ba suda wasu dokoki da suke jagorantar rayuwarsu. Babu wani tunanin da za ta yi na abinda ya wuce ta yi nadama; haka nan, babu wani tunani da za ta yi na abinda zai zo nan gaba, ta shiga wani hali. Ka gani ita abinda ta sani, shi ne ta samu ta ci to godewa, wanda ya ba ta shikenan.
Saboda, shi mutum, wanda aka halitta a bisa kyakkyawan tsari, idan har tunaninsa zai tsaya ne game da duniya, kawai, to sai ya koma mafi ƙasƙantar maƙasƙanta sai ya koma tsuntsu da dabba duk sun fi shi daraja.
Na yi bayanin wannan sosai a wani wuri ta hanyar bada misah:
Wani mutum da yaran gidansa guda biyu, sai ya ɗauki naira ɗari ya ba ɗaya ya ce ya sayo masa yadi, ya kawo naira dubu ya ba na biyun ya ce shi ma ya sayo masa yadi. Kowannensu ya tafi kasuwa. Mai Naira dari ya sayo kyakkyawan yadi; mai Naira dubu ko da yake wawane ya je ya mika kuɗinj kawai ga mai kaya ya ce ya ba shi yadi. Abinka da mutumin yau, ganin mai sayen yadi sakarai ne, sai mai kaya ya ɗauko yadin da ko kare baya sa ba ya ba shi.
Wanda aka aika da Naira ɗari, yana zuwa, ga mai gidansa, sai yabo da san-barka. Mai Naira dubu kuwa, ai sai zagi da tsinuwa kai har ma da duka.
Me yasa haka ta faru? Saboda ko sakarai ya san cewa, Naira dubu ta fi gaban ta kare a abinda ko kare ba zai ci ba.
To haka ma ga abubuwan halitttan biyu: mutum da dabba. Mutum ya ɗaran ma dabba nesa ba kusa ba ta kowanne fanni. Duba fa, mutum ne ke iya gane abu mai ƙyau, ya kuma rarrabe tsakanin mai daɗi da mara daɗi ta hanyar ɗannano, ya kuma tsaya tsam ya yi tunanin me ya ke so, me kuma ya dace da shi? Dabba fa? Ina! Ai ko kusa ba ta kai nan ba. Abinda take iya yi kawai shi ne gani da ido wani lokaci, da ɗanɗano, shi kenan kawai!
Shin ka taɓa tsayawa ka, tambayi kanka: me yasa mutum ne kawai aka sani da dukiya?
Ga Amsa:
Mutum shi ke da tunani da hangen nesa, shi kuma ke da ji da gani, kuma shi ke da guri/buri da kwaɗayi. Saboda wannan yanayi nasa, sai ya kasance buƙatunsa da aikace-aikacensa sun faɗaɗa, sun kai inda suka kai. Kuma shi da ma an halitta shi kusan daidai da waɗannan abubuwa, sai Allah mahaliccinsa ya kai shi wani matsayin kusa da kamata, amma da saura. Kamar dai yadda ake cewa: “Ɗan adam tara yake, bai cika goma ba.”
To fa wannan da aka yiwa ɗan adam, ba wai don duniya kawai aka yi ta ba har ma da lahira. Ɗan adam yana neman lahira ta hanyar bauta, kaskantar da kai da ƙwaɗayi ga Allah, mai Rahama mai jin kai.
Saboda haka, ya kai ɗan adam wanda ya sa duniya a gaba, wanda bai kula da abinda ake cewa “mafi kyakkyawan tsari na yadda aka halitta shi ba, to tsoron ƙwanuka, babu abinda bai gani ba na rayuwa. Saboda haka kula da wannan misali da zai buga maka:
Ni ne na tashi zan yi wata doguwar tafiya. Sai mai gida na ya ɗauko wasu ‘yan kuɗi daga cikin tarina, ya ba ni, sai na kama hanya. Ina ta tafiya, har na isa birini, isata . ke da wuya, sai na ɓannatar da kudin nan tas! Ni da ma ba ni rike da wani abu, na sayarwa ko na guzuri. Saboda haka ɓannatar da kudina sai na zauna ba sisi, sai baƙin ciki da nadama.
Ina cikin wannan hali sai ga wani mutum ya zo ya ce mani:
“Ka almubazzarantar da ƙudinka! Yanzu babu abinda ya cancance ka, sai horo. Yanzu dai hakan nan hannu biyu za ka isa inda za ka. Amma da kai wani ne da sai ka koma ka karbo abinda ya ragu, ka ɗan kukkulla ka samu abin buƙata. Can inda za ka.”
Na tsaya na yi tunani, na ga ban iyawa. Ganin haka niutunin nan ya ce, “ka kwatanta.” Amma ina! Zuciyata ta dai bata ba ni. Ya dai ƙara Magana. Amma ina! Zuciyata ta nisa. Ganin haka, sai ya yi fushi, ya kama gabansa.
Wucewarsa ke da wuya, sai al’amarni ya canza. Sai ga ni cikin jirgi. Sai na tsirata. Ga furanni masu ƙamshi ta kowane ɓangare. Abinka da wanɗa bai sani ba, sai na miƙa hannu zan ciro furannin nan. Miƙa hannu ke da wuya, ashe duk ƙaya ne jikinsu, saboda haka, sai suka kakkarce mani, hannu suna ta jinni. Sai mai kula da jirgi ya ce da ni:
“Idan kana son furannin nan, kawo kuɗi in ba ka. Ka ga yanzu ga raunin da ka yi, gas hi kuma hukunci na jiranka, don ka yi kokarin dibar su, ba are da izini ba.”
Cikin haushi, sai na leka ta taga in ga shin mun kusa kaiwa. Haba ai sai naga can gabanmu, ramuka ne, sai jefa mutane a ke ciki. Ashe kaburbura ne, hangawan nan da zan yi, sai na hango wani ƙaɓari ɗauke da sununa” SAID. Haba ai sai na niɗe. Zuwa can, sai na ji muryan mutumin nan farko da ya ba ni shawara yana cewa: “Yanzu ka dawo cikin hakalin ka ko?”
Na ce, “I amma ai a banza.” Sai ya ce: “a’a, ba’a banza ba ne, nemi gafarar Ubangijinka ka kuma dogara gare shi ka gani.” Na ce masa to! Zan yi yadda ya ce. Shi ke nan!
Ashe mafarki ne, sai kawai na farka. Allah dai yasa ya zama mani alheri.
Yanzu ni zan fassara wani ko wasu sassa na mafarkin kai kuma ka fassara sauran.
Doguwar tafiya da na ce na yi, na nuffin haihuwar mutum, har zuwa ga yaranta, da tsufa da kuma komawa zuwa ga kabari, har zuwa tada mutum, da kuma tsallake siraɗi.
‘yan kuɗai da na rike kuwa, kwatankwacin yawan shekarun da mutum zai yi ne. ina ganin na yi wannan mafarki in a ɗan shekara arba’in da biyar ‘yan kuɗin da na ce sun kai Naira goma sha biyar. Wani masanin Kur’ani ya shawarce ni cewa in ɗauki kowace Naira a matsayin shekara, saboda haka, saura shekaru goma sha biyar suka rage mani a duniya. Birnin da na je kuma, cikin duniya jirgin da na shiga shi ne zamani, furannin kuwa masu kanshi da banshawa, masu ƙaya su ne hane- hane na rayuwa, idan mutum ya ce, sai ya same su, ya sha wahala, idan ko ya yi haƙuri, ya tsira. A takaice dai, ma’anar wanna mafarki shi ne samun jin daɗi da more rayuwa ta hanyar da Allah ya tsara ya isar ma ɗan adam. Babu buƙatar mutum ya ce zai same su ko ta halin ƙaƙa. Na bar maka fassarar sauran.
DÖRDÜNCÜ NÜKTE
İnsan, şu kâinat içinde pek nazik ve nâzenin bir çocuğa benzer. Zaafında büyük bir kuvvet ve aczinde büyük bir kudret vardır. Çünkü o zaafın kuvvetiyle ve aczin kudretiyledir ki şu mevcudat ona musahhar olmuş. Eğer insan zaafını anlayıp kālen, halen, tavren dua etse ve aczini bilip istimdad eylese; o teshirin şükrünü eda ile beraber matlubuna öyle muvaffak olur ve maksatları ona öyle musahhar olur ki iktidar-ı zatîsiyle onun öşr-i mi’şarına muvaffak olamaz. Yalnız bazı vakit lisan-ı hal duasıyla hasıl olan bir matlubunu yanlış olarak kendi iktidarına hamleder. Mesela, tavuğun yavrusunun zaafındaki kuvvet, tavuğu arslana saldırtır. Yeni dünyaya gelen arslanın yavrusu, o canavar ve aç arslanı kendine musahhar edip onu aç bırakıp kendi tok oluyor. İşte cây-ı dikkat zaaftaki bir kuvvet ve şâyan-ı temaşa bir cilve-i rahmet…
Nasıl ki nazdar bir çocuk ağlamasıyla ya istemesiyle ya hazîn haliyle matlublarına öyle muvaffak olur ve öyle kavîler ona musahhar olurlar ki o matlublardan binden birisine bin defa kuvvetçiğiyle yetişemez. Demek zaaf ve acz, onun hakkında şefkat ve himayeti tahrik ettikleri için küçücük parmağıyla kahramanları kendine musahhar eder. Şimdi böyle bir çocuk, o şefkati inkâr etmek ve o himayeti ittiham etmek suretiyle ahmakane bir gurur ile “Ben kuvvetimle bunları teshir ediyorum.” dese, elbette bir tokat yiyecektir.
İşte insan dahi Hâlık’ının rahmetini inkâr ve hikmetini ittiham edecek bir tarzda küfran-ı nimet suretinde Karun gibi اِنَّمَٓا اُوتٖيتُهُ عَلٰى عِل۟مٍ yani “Ben kendi ilmimle, kendi iktidarımla kazandım.” dese, elbette sille-i azaba kendini müstahak eder.
Demek şu meşhud saltanat-ı insaniyet ve terakkiyat-ı beşeriye ve kemalât-ı medeniyet; celb ile değil, galebe ile değil, cidal ile değil, belki ona, onun zaafı için teshir edilmiş, onun aczi için ona muavenet edilmiş, onun fakrı için ona ihsan edilmiş, onun cehli için ona ilham edilmiş, onun ihtiyacı için ona ikram edilmiş. Ve o saltanatın sebebi, kuvvet ve iktidar-ı ilmî değil, belki şefkat ve re’fet-i Rabbaniye ve rahmet ve hikmet-i İlahiyedir ki eşyayı ona teshir etmiştir. Evet, bir gözsüz akrep ve ayaksız bir yılan gibi haşerata mağlup olan insana, bir küçük kurttan ipeği giydiren ve zehirli bir böcekten balı yediren; onun iktidarı değil, belki onun zaafının semeresi olan teshir-i Rabbanî ve ikram-ı Rahmanîdir.
Ey insan! Madem hakikat böyledir, gururu ve enaniyeti bırak. Uluhiyetin dergâhında acz ve zaafını, istimdad lisanıyla; fakr ve hâcatını, tazarru ve dua lisanıyla ilan et ve abd olduğunu göster. Ve حَس۟بُنَا اللّٰهُ وَنِع۟مَ ال۟وَكٖيلُ de, yüksel.
Hem deme ki: “Ben hiçim, ne ehemmiyetim var ki bu kâinat bir Hakîm-i Mutlak tarafından kasdî olarak bana teshir edilsin, benden bir şükr-ü küllî istenilsin?”
Çünkü sen, çendan nefsin ve suretin itibarıyla hiç hükmündesin. Fakat vazife ve mertebe noktasında, sen şu haşmetli kâinatın dikkatli bir seyircisi, şu hikmetli mevcudatın belâgatlı bir lisan-ı nâtıkı ve şu kitab-ı âlemin anlayışlı bir mütalaacısı ve şu tesbih eden mahlukatın hayretli bir nâzırı ve şu ibadet eden masnuatın hürmetli bir ustabaşısı hükmündesin.
Evet ey insan! Sen, nebatî cismaniyetin cihetiyle ve hayvanî nefsin itibarıyla sağir bir cüz, hakir bir cüz’î, fakir bir mahluk, zayıf bir hayvansın ki bütün dehşetli mevcudat-ı seyyalenin dalgaları içinde çalkanıp gidiyorsun. Fakat muhabbet-i İlahiyenin ziyasını tazammun eden imanın nuruyla münevver olan İslâmiyet’in terbiyesiyle tekemmül edip; insaniyet cihetinde, abdiyetin içinde bir sultansın ve cüz’iyetin içinde bir küllîsin, küçüklüğün içinde bir âlemsin ve hakaretin içinde öyle makamın büyük ve daire-i nezaretin geniş bir nâzırsın ki diyebilirsin: “Benim Rabb-i Rahîm’im dünyayı bana bir hane yaptı. Ay ve güneşi, o haneme bir lamba; ve baharı, bir deste gül; ve yazı, bir sofra-i nimet; ve hayvanı, bana hizmetkâr yaptı. Ve nebatatı, o hanemin ziynetli levazımatı yapmıştır.”
Netice-i kelâm: Sen eğer nefis ve şeytanı dinlersen esfel-i safilîne düşersin. Eğer Hak ve Kur’an’ı dinlersen a’lâ-yı illiyyîne çıkar, kâinatın bir güzel takvimi olursun.
BEŞİNCİ NÜKTE
İnsan, şu dünyaya bir memur ve misafir olarak gönderilmiş, çok ehemmiyetli istidat ona verilmiş. Ve o istidadata göre ehemmiyetli vazifeler tevdi edilmiş. Ve insanı, o gayeye ve o vazifelere çalıştırmak için şiddetli teşvikler ve dehşetli tehditler edilmiş. Başka yerde izah ettiğimiz vazife-i insaniyetin ve ubudiyetin esasatını şurada icmal edeceğiz. Tâ ki “ahsen-i takvim” sırrı anlaşılsın.
İşte insan, şu kâinata geldikten sonra iki cihet ile ubudiyeti var: Bir ciheti; gaibane bir surette bir ubudiyeti, bir tefekkürü var. Diğeri; hazırane, muhataba suretinde bir ubudiyeti, bir münâcatı vardır.
Birinci vecih şudur ki: Kâinatta görünen saltanat-ı rububiyeti, itaatkârane tasdik edip kemalâtına ve mehasinine hayretkârane nezaretidir.
Sonra, esma-i kudsiye-i İlahiyenin nukuşlarından ibaret olan bedî’ sanatları, birbirinin nazar-ı ibretlerine gösterip dellâllık ve ilancılıktır.
Sonra, her biri birer gizli hazine-i maneviye hükmünde olan esma-i Rabbaniyenin cevherlerini idrak terazisiyle tartmak, kalbin kıymet-şinaslığı ile takdirkârane kıymet vermektir.
Sonra, kalem-i kudretin mektubatı hükmünde olan mevcudat sahifelerini, arz ve sema yapraklarını mütalaa edip hayretkârane tefekkürdür.
Sonra, şu mevcudattaki ziynetleri ve latîf sanatları istihsankârane temaşa etmekle onların Fâtır-ı Zülcemal’inin marifetine muhabbet etmek ve onların Sâni’-i Zülkemal’inin huzuruna çıkmaya ve iltifatına mazhar olmaya bir iştiyaktır.
İkinci vecih, huzur ve hitap makamıdır ki eserden müessire geçer, görür ki: Bir Sâni’-i Zülcelal, kendi sanatının mu’cizeleri ile kendini tanıttırmak ve bildirmek ister. O da iman ile marifet ile mukabele eder.
Sonra görür ki bir Rabb-i Rahîm, rahmetinin güzel meyveleriyle kendini sevdirmek ister. O da ona hasr-ı muhabbetle, tahsis-i taabbüdle kendini ona sevdirir.
Sonra görüyor ki bir Mün’im-i Kerîm, maddî ve manevî nimetlerin lezizleriyle onu perverde ediyor. O da ona mukabil; fiiliyle, haliyle, kāliyle, hattâ elinden gelse bütün hâsseleri ile cihazatı ile şükür ve hamd ü sena eder.
Sonra görüyor ki bir Celil-i Cemil, şu mevcudatın âyinelerinde kibriya ve kemalini ve celal ve cemalini izhar edip nazar-ı dikkati celbediyor. O da ona mukabil, “Allahu ekber, Sübhanallah” deyip mahviyet içinde hayret ve muhabbet ile secde eder.
Sonra görüyor ki bir Ganiyy-i Mutlak, bir sehavet-i mutlak içinde nihayetsiz servetini, hazinelerini gösteriyor. O da ona mukabil, tazim ve sena içinde kemal-i iftikar ile sual eder ve ister.
Sonra görüyor ki o Fâtır-ı Zülcelal, yeryüzünü bir sergi hükmünde yapmış. Bütün antika sanatlarını orada teşhir ediyor. O da ona mukabil, “Mâşâallah” diyerek takdir ile “Bârekellah” diyerek tahsin ile “Sübhanallah” diyerek hayret ile “Allahu ekber” diyerek istihsan ile mukabele eder.
Sonra görüyor ki bir Vâhid-i Ehad, şu kâinat sarayında taklit edilmez sikkeleriyle, ona mahsus hâtemleriyle, ona münhasır turralarıyla, ona has fermanlarıyla bütün mevcudata damga-i vahdet koyuyor ve tevhidin âyâtını nakşediyor. Ve âfak-ı âlemin aktarında vahdaniyetin bayrağını dikiyor ve rububiyetini ilan ediyor. O da ona mukabil, tasdik ile iman ile tevhid ile iz’an ile şehadet ile ubudiyet ile mukabele eder.
İşte bu çeşit ibadat ve tefekküratla hakiki insan olur, ahsen-i takvimde olduğunu gösterir. İmanın yümnüyle emanete lâyık, emin bir halife-i arz olur.
Ey ahsen-i takvimde yaratılan ve sû-i ihtiyarıyla esfel-i safilîn tarafına giden insan-ı gafil! Beni dinle. Ben de senin gibi gençlik sarhoşluğuyla gaflet içinde dünyayı hoş ve güzel gördüğüm halde, gençlik sarhoşluğundan ihtiyarlık sabahında ayıldığım dakikada, o güzel zannettiğim âhirete müteveccih olmayan dünyanın yüzünü nasıl çirkin gördüğümü ve âhirete bakan hakiki yüzü ne kadar güzel olduğunu, On Yedinci Söz’ün İkinci Makamı’nın 233-234’üncü sahifelerinde yazılan iki levha-i hakikate bak, sen de gör:
Birinci Levha: Ehl-i dalalet gibi fakat sarhoş olmadan gaflet perdesiyle eskiden gördüğüm ehl-i gaflet dünyasının hakikatini tasvir eder.
İkinci Levha: Ehl-i hidayet ve huzurun hakikat-i dünyalarına işaret eder. Eskiden ne tarzda yazılmış, o tarzda bıraktım. Şiire benzer fakat şiir değillerdir.
سُب۟حَانَكَ لَا عِل۟مَ لَنَٓا اِلَّا مَا عَلَّم۟تَنَٓا اِنَّكَ اَن۟تَ ال۟عَلٖيمُ ال۟حَكٖيمُ
رَبِّ اش۟رَح۟ لٖى صَد۟رٖى وَيَسِّر۟ لٖٓى اَم۟رٖى وَاح۟لُل۟ عُق۟دَةً مِن۟ لِسَانٖى يَف۟قَهُوا قَو۟لٖى
اَللّٰهُمَّ صَلِّ وَ سَلِّم۟ عَلَى الذَّاتِ ال۟مُحَمَّدِيَّةِ اللَّطٖيفَةِ ال۟اَحَدِيَّةِ شَم۟سِ سَمَاءِ ال۟اَس۟رَارِ وَ مَظ۟هَرِ ال۟اَن۟وَارِ وَ مَر۟كَزِ مَدَارِ ال۟جَلَالِ وَ قُط۟بِ فَلَكِ ال۟جَمَالِ اَللّٰهُمَّ بِسِرِّهٖ لَدَي۟كَ وَ بِسَي۟رِهٖ اِلَي۟كَ اٰمِن۟ خَو۟فٖى وَ اَقِل۟ عُث۟رَتٖى وَ اَذ۟هِب۟ حُز۟نٖى وَ حِر۟صٖى وَ كُن۟ لٖى وَ خُذ۟نٖى اِلَي۟كَ مِنّٖى وَ ار۟زُق۟نِى ال۟فَنَاءَ عَنّٖى وَ لَا تَج۟عَل۟نٖى مَف۟تُونًا بِنَف۟سٖى مَح۟جُوبًا بِحِسّٖى وَاك۟شِف۟ لٖى عَن۟ كُلِّ سِرٍّ مَك۟تُومٍ يَا حَىُّ يَا قَيُّومُ يَا حَىُّ يَا قَيُّومُ يَا حَىُّ يَا قَيُّومُ وَ ار۟حَم۟نٖى وَار۟حَم۟ رُفَقَائٖى وَ ار۟حَم۟ اَه۟لَ ال۟اٖيمَانِ وَ ال۟قُر۟اٰنِ اٰمٖينَ يَا اَر۟حَمَ الرَّاحِمٖينَ وَ يَا اَك۟رَمَ ال۟اَك۟رَمٖينَ
وَ اٰخِرُ دَع۟وٰيهُم۟ اَنِ ال۟حَم۟دُ لِلّٰهِ رَبِّ ال۟عَالَمٖينَ